Bincika gaskiya: Yadda rade-radin wanke Abba Kyari yake, tare da dawo dashi bakin aiki

Bincika gaskiya: Yadda rade-radin wanke Abba Kyari yake, tare da dawo dashi bakin aiki

Wasu mutane na ta yada hotuna da rubutu cewa, rundunar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki, to amma ya gaskiyar batun yake? An bincika gaskiyar lamarin don kaucewa jita-jita.

A karshen mako ne rahotanni da dama a shafukan sada zumunta da suka yi ikirarin cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta mayar da Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar bakin aikinsa.

Sanarwar ta kuma ce an wanke Kyari daga dukkan zarge-zargen da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta yi masa kan hannu a damfara da Hushpuppi ya tafka a kasar Qatar.

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?
Abba Kyari lokacin murnar kame Evans | Hoto: tori.ng
Asali: UGC

Wasu daga cikin rahotannin sun kai ga cewa an tura Kyari jihar Anambra domin aiki wajen zaben gwamna a ranar 6 ga watan Nuwamba a matsayin aikinsa na farko bayan dage dakatarwar da aka yi masa.

Kara karanta wannan

Yadda Tarayyar Turai ta kashe £130m wajen tallafawa 'yan gudun hijira a Borno

A shafin sada zumunta, wani mai suna Gold Myne TV, mai mabiya kusan 44,000 ya yada rubutu tare da wani hoto da ke ikirarin cewa an "sake dawo da" Kyari wanda har haka ya haifar da "ji dadi da murna".

Rubutun ya kara da cewa:

"Farin ciki yayin da mukaddashin 'yan sanda ya ba DCP kuma abokin Hushpuppi, Abba Kyari da aka dakatar, damar ci gaba da aiki a matsayin jami'i."
Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?
Daya daga cikin rubuce-rubucen karya | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

An yada rubutun ne a ranar Asabar kuma ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ya samar da sake yadawa 335, dankwale 143 da kuma sharhi 82.

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?
Wani rubutun na daban | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?
Wani rubutun na daban | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Bayani tun farko

A watan Yuli, FBI ta bayyana yadda aka zargi Kyari da hada baki da Hushpuppi wajen daure daya daga cikin abokan harkallar Hushpuppi bayan takaddama kan badakalar dala miliyan 1.1 kan wani balarabe dan kasuwar kasar Qatar.

Kara karanta wannan

Kano: Hotunan bata gari 59 da aka kama kan zargin fashi, safarar miyagun ƙwayoyi da makaman da aka ƙwato hannunsu

Hukumar ta FBI ta kuma yi zargin cewa Hushpuppi ya aike da kudi ga masu binciken ta wani asusun banki tare da karbar bakuncin Kyari a gidansa na Dubai.

Bayan wannan zargi, an dakatar da babban jami’in inda aka kafa kwamiti don gudanar da bincike kan zargin da hukumar ta FBI ke yi masa. Sai dai, Kyari ya musanta zargin, yana mai cewa "hannayensa a tsaftace suke".

Batun ya haifar da rudani da dama a kafafen sada zumunta da zagayen yanar gizo, wasu daga cikinsu tuni an binciko gaskiyarsu da tushensu.

Tantance gaskiya

Don tantance gaskiyar batun, jaridar TheCable ta binciki tushen hoton da aka yi amfani da shi don yada labarin ta hanyar juya binciken hoton akan kafafen bincike da yawa.

A wannan hoton dai wasu mutane ne suka daga Kyari a wani yanayi na shagalin biki.

Da farko an buga hoton ne bisa ga bincike akan gidan shafin yanar gizon labarai na Tori a ranar 12 ga watan Yuni, 2017

Kara karanta wannan

Hush-Kyari: Saura kiris duniya ta san makomar Abba Kyari, FDC zai ba da rahoto

A cikin labarin, an yaba wa Kyari ne bisa jarumtar da ya yi wajen kame Chukwudimeme Onwuamadike, wanda ake zargi da satar mutane da aka fi sani da Evans. Har ila yau, ya kara da cewa "jarumin dan sandan" abokan aikinsa ne suka daga shi don murnar kama Evans.

Har ila yau, bitar rahotanni a yanar gizo ya nuna cewa, babu wata kafar yada labarai mai inganci da ta wallafa rahoton cewa an mai da Kyari bakin aiki.

Sai dai jaridar Punch a wani rahoto da ta fitar ta ce majiyoyin ‘yan sanda sun tabbatar da cewa har yanzu Kyari na kan dakatarwa. Wato babu wata shaida a bainar jama'a cewa an dage dakatarwar da aka yi wa Kyari.

Jaridar TheCable ta tuntubi Frank Mba, mai magana da yawun 'yan sanda, don jin ta bakinsa, amma bai amsa kiran waya ba da sakonnin tes.

Hukunci kan batun

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

Babu isasshiyar shaida da ke tabbatar da ikirarin cewa hukumomin 'yan sanda sun maido da Kayri bakin aiki. Don haka, da'awar cewa an dage dakatarwar tsagoron karya ce da ake yadawa a kafafen sada zumunta.

Hush-Kyari: Saura kiris duniya ta san makomar Abba Kyari, FDC zai ba da rahoto

A wani labarin, Punch ta ruwaito cewa, makomar tsohon kwamandan tawagar IRT ta 'yan sanda, Abba Kyari, na nan tafe, a daidai lokacin da hukumar ‘yan sanda ke jiran shawarwarin kwamitin ladabtarwa na rundunar ‘yan sanda kan shari’ar sa.

An tattaro cewa shawarwarin FDC za su kasance jigon hukuncin da hukumar za ta yanke tare da tabbatar da makomar Kyari a aikin dan sandan Najeriya.

Kwanakin baya rahotanni sun bayyana cewa, Sufeto Janar na 'yan sanda ya mika bayanan bincike kan zargin Abba Kyari da hannu a cikin badakalar dala miliyan 1.1 kan wani balarabe tare da Hushpuppi ga ministan shari'a Abubakar Malami (SAN).

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

Asali: Legit.ng

Online view pixel