Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da kisan rayuka 6 da miyagu suka yi a karamar hukumar Omala ta jihar Kogi
  • Miyagun sun shiga fadar basarake Anyebe Salifu inda suka kone ta tare da harbe mutane 3 har lahira a take
  • 'Yan bindigan sun kara da banka wa wasu gidajen wuta tare da kashe wasu mutum 3 wurin karfe 7 na safiyar Litinin

Omala, Kogi - Rundunar 'yan sandan jihar Kogi a ranar Laraba sun tabbatar da kisan gillar da wasu miyagun 'yan bindiga suka yi wa mutum shida tare da banka wa wasu gidaje wuta a ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, mummunan lamarin ya auku ne a yankin Bagana da ke karamar hukumar Omala da ke jihar Kogi.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kogi, Idrisu Dabban, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin bayan ziyartar yankin da yayi, ya ce an dauka matakan da suka dace wurin dakile sake faruwar al'amarin.

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka gidaje masu yawa
Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka gidaje masu yawa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya tattaro cewa, maharan sun je kai tsaye fadar Sarki Anyebe Salifu, wanda shi ne mai sarauta da ke da daraja ta uku a yankin.

Wani ganau ba jiyau ba mai suna Yakubu Salifu, wanda kuma da ne ga basaraken, ya ce miyagun sun tsinkayi yankin wurin karfe 7 da rabi na safe.

A wannan lokacin kuwa, da yawa daga cikin matasan yankin sun tafi gona kuma kai tsaye suka shiga fadar basaraken, Daily Trust ta wallafa.

An gano cewa, miyagun sun banka wa fadar wuta a lokacin da suka kai farmakin, a take kuma suka harbe mutum 3 har da wata mata mai suna Achebe Alih.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Shugaban 'yan bindiga, Shehu Rekeb, ya sanar da dalilinsu na kai farmakin Goronyo

A wani labari na daban, 'yan bindiga da ke karakaina tsakanin jihohin Sokoto zuwa Zamfara sun dauka alhakin kai farmakin kasuwar Goronyo a jihar Sokoto inda suka halaka rayuka 49 a ranar Lahadin da ta gabata.

Daya daga cikin gagararrun 'yan bindigan da ke da kusanci da Kachallah Turji da Halilu Sububu, manyan miyagun yankin, mai suna Shehu Rekeb, ya ce sun kai wannan farmakin ne domin daukar fansa kan kisan Fulani da ake yi a yankin.

A ranar Talatar da ta gabata Daily Trust ta ruwaito cewa, farmakin na hadin guiwa ne saboda yadda sama da babura dari suka tsinkayi kasuwar kuma suka bude wa jama'ar wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel