Yadda Tarayyar Turai ta kashe £130m wajen tallafawa 'yan gudun hijira a Borno

Yadda Tarayyar Turai ta kashe £130m wajen tallafawa 'yan gudun hijira a Borno

  • An kaddamar da wani shirin fim mai suna HOPE, wanda ya bayyana yadda rikicin Boko Haram ya illata mutanen Borno
  • A wurin taron, wakilan EU sun bayyana irin gudunmawar da suka bayar wajen dakike rikice-rikice da kuma tallafawa 'yan gudun hijira a Borno
  • Hakazalika, EU ta bayyana irin makudan kudaden da ta kashe domin tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya taba

Abuja - Kungiyar Tarayyar Turai ta hanyar shirye-shiryenta na tallafi ta farfado da rayuwar miliyoyin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihohin Borno da Arewa maso Gabas, in ji shugabar tawagarta a Najeriya da ECOWAS, Ambasada Samuela Isopi.

Ta ce kungiyar ta EU ta bada kudi kusan Yuro miliyan 130 a cikin shekaru hudu da suka gabata don tallafawa kokarin gwamnatin jihar Borno na sake ginawa da kuma gyara al’ummomin da abin ya shafa, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jami’o’i da manyan makarantu 30 da Shugaba Buhari ya kirkira daga 2015 zuwa 2021

Wannan tallafin kudade kadai, a cewarta, ya taimaka wajen maido da ababen more rayuwa a fannoni da yawa.

Yadda Tarayyar Turai ta kashe £130m wajen tallafawa 'yan gudun hijira a Borno
Taswirar jihar Borno | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewarta, fannonin sun hada da kiwon lafiya da abinci mai gina jiki, noma, ruwa da tsaftar muhalli, kare al’umma, ilimi, magance rikice-rikice da hadin kai a tsakanin al’ummomin da suka rasa matsugunansu da kuma al’ummomin da suka karbi bakuncinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami’in kungiyar ta EU ya yi wannan jawabi ne a lokacin bikin kaddamar da wani shirin fim mainsuna HOPE kan gwagwarmayar ‘yan gudun hijira a jihar da aka gudanar a cibiyar Musa Yar’Adua da ke Abuja.

Isopi ta ce ta hanyar tallafin kudade a cikin shekaru hudu da suka gabata a yankunan da rikici ya shafa a Borno, EU ta ba da gudummawa wajen dawo da zaman lafiya tare da dawo da fata ga miliyoyin jama'a a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun manta Allah: Buhari ya bayyana mafita ga matsalolin Najeriya

Bugu da kari, ta ce, kungiyar ta EU, tun daga shekarar 2014 ta ke samar da makudan kudade domin tallafawa 'yan gudun hijira.

Ta kara da cewa:

"Mun yi farin cikin ganin cewa tallafin ya dawo da fata a jihar Borno yayin da miliyoyin mutane ke komawa garuruwansu."

Da take jaddada makasudin shirya shirin, jakadar ta ce an yi shi ne domin wayar da kan al’ummar Turai da Najeriya kan illar tashe-tashen hankula da matsalolin tsaro da ke addabar al’ummar jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Bugu da kari, fim din ya nuna irin rawar da kungiyar ta EU ke takawa, da irin gudunmawar da take bayarwa wajen bayar da agajin jin kai da farfado da al'ummar da ke fama da rikici, tare da hadin gwiwarta da gwamnatin Najeriya.

Kungiyoyin waje na ci gaba da tallafawa'yan gudun hijira a yankunan da rikicin Boko Haram ya rutsa dasu, kasancewar jihar ta Borno ta sha fama da addabar 'yan Boko Haram.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha

A watan Satumba, UNICEF ta ce ta mayar da yaran da basa zuwa makaranta sama 5000 zuwa makarantu domin su ci gaba da karatu, Punch ta ruwaito.

ISWAP sun kai hari kan 'yan Boko Haram

A baya kadan, Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa an kashe manyan jiga-jigan kungiyar Boko Haram guda biyu, Amir Modou Marte da Amir Moustapha Baga.

An kawar da su ne a wani kwanton bauna da mayakan abokan hamayyarsu na ISWAP suka yi a ranar Lahadi 24 ga watan Oktoba.

An tattaro cewa wasu 'yan ta'adda 15 na daga cikin wadanda kungiyar Boko Haram ta kashe a lokacin kwanton baunar da suka yi a Toumboun Gadura'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel