Kano: Hotunan ɓata gari 59 da aka kama kan zargin fashi, safarar miyagun ƙwayoyi da makaman da aka ƙwato

Kano: Hotunan ɓata gari 59 da aka kama kan zargin fashi, safarar miyagun ƙwayoyi da makaman da aka ƙwato

  • Yan sanda a jihar Kano sun yi nasarar kama wasu mutane 59 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban
  • Daga cikinsu akwai wadanda ake zargi da aikata fashi da makami, mallakar kayan sata, ta'amulli da miyagun kwayoyi ds
  • DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar

Kano - Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Kano ta ce ta kama mutum 59 da ake zargin masu laifi ne kuma ta kwato makamai da muggan kwayoyi a hannunsu, rahoton Daily Trust.

Hakan na zuwa ne yayin da kwamishinan yan sandan jihar, Sumaila Shuaibu Dikko ke cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin yaki da 'yan daba.

Kara karanta wannan

Borno: Dakarun soji sun halaka 'yan ta'adda masu hada bam daga takin zamani

Kano: Ƴan sanda sun kama ɓata gari 59, sun ƙwato muggan makamai da ƙwayoyi
'Yan sanda sun kama ɓata gari 59, sun ƙwato muggan makamai da ƙwayoyi a Kano. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kano: Ƴan sanda sun kama ɓata gari 59, sun ƙwato muggan makamai da ƙwayoyi
Bata garin da aka kama bisa zargin aikata laifuka a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kano: Ƴan sanda sun kama ɓata gari 59, sun ƙwato muggan makamai da ƙwayoyi
'Yan sanda sun kama ɓata gari 59, sun ƙwato muggan makamai da ƙwayoyi a jihar Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce:

"An kama wadanda ake zargin ne daga 19/10/2021 zuwa 27/10/2021, cikinsu akwai wadanda ake zargi da fashi da makami sata da kuma ta'amulli da miyagun kwayoyi."

Hakazalika, ya ce dukkan wadanda ake zargin da aka kama mazauna Kano ne, wasunsu an kama su da makamai da kayan sata.

Kwamishinan yan sandan Kano, CP Dikko ya yi kira ga dukkan bata garin da masu ta'amulli da miyagun kwayoyin su tuba su sauya halayensu ko kuma su bar jihar domin za su shigo hannu kuma za a hukunta su.

Kano: Ƴan sanda sun kama ɓata gari 59, sun ƙwato muggan makamai da ƙwayoyi
Wasu daga cikin wadanda aka kama bisa aikata laifuka a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kwamishinan ya mika godiyarsa ga al'ummar Kano saboda hadin kai da goyon baya da suke bawa rundunar. Ya bukaci su cigaba da yi wa jihar da kasa addu'a.

Kara karanta wannan

Dogo Giɗe, hatsabibi shugaban ƴan bindiga ya haramta shan giya da kayan maye a wasu ƙauyukan Zamfara

Za kuma a gurfanar da su gaban kuliya su girbi abin da suka shuka da zarar an kammala bincike.

Kano: 'Yan Hisbah sun kama matashin da ya yi yunkurin sayar da kansa kan N20,000,000

A wani rahoton, Rundunar ‘yan sandan musulunci ta Hisbah a jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 26 da ya sa kan sa a kasuwa.

A wata tattaunawa da BBC Pidgin ta yi da kwamanda janar na rundunar, Sheikh Harun Ibn-Sina ya bayyana hakan.

Ibn-Sina ya ce sun kama matashin ne saboda abinda ya aikata ya ci karo da koyarwar addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel