Sojoji sun damke Karime, matar rikakken dan bindiga Zubairu da Malaminsu, Idris Audu

Sojoji sun damke Karime, matar rikakken dan bindiga Zubairu da Malaminsu, Idris Audu

  • Sojojin Najeriya sun yi wa 'yan bindiga lugude a jihar Kaduna inda suka tarwatsa wasu sansanonin miyagun
  • A wannan halin ne suka cafke Malam Idris Audu, malamin 'yan bindigan da kuma Karime, matar gagararren dan bindiga Zubairu
  • Dakarun sun yi nasarar cafke wasu mutum 2 da ake zargi da hada kai da 'yan bindigan tare da kwace wasu miyagun makamai

Kaduna - Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindigan daji tare da tarwatsa sansanoninsu a wani samamen da suka kai kananan hukumomin Igabi da Chikun na jihar Kaduna.

Dakarun sojin sun cafke wani Malam Idris Audu, babban malamin 'yan bindigan da wata Rabi Hajiya Karime, wacce aka gano ita ce matar gagararren dan bindiga, Zubairu.

Sojoji sun damke Karime, matar rikakken dan bindiga Zubairu da Malaminsu, Idris Audu
Sojoji sun damke Karime, matar rikakken dan bindiga Zubairu da Malaminsu, Idris Audu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a wata takarda ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Sojoji sun halaka 'yan bindiga yayin da "dogarin Biafra" suka kai musu farmaki a Abia

Ya kara da cewa, an cafke wani Abdulrasheed Gambo Na Halima da Abubakar Idris Na Halima sakamakon zarginsu da ake da bai wa 'yan bindiga gudumawa.

Aruwan ya ce dakarun sojin sun kai samamen ne a Faka, Katuka, Barebari da Maguzawa.

Ya bayyana cewa, an hango wasu 'yan bindiga masu tarin yawa a kusa da rafin Maguzawa inda ya ce, "dakarun sojin saman Najeriya da ke cikin jirgi mai saukar ungulu ne suka bude musu wuta tare da halaka su."

Ya ce jami'an tsaron sun yi sintiri a Katuka, kusan kilomita tara daga Kangon Kadi da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna. A nan suka ci karo da dan bindiga 1 wanda suka cafke.

Aruwan ya kara da cewa sun yi nasarar samo wasu babura, bindiga kirar AK47, harsasan AK47, makamai da kuma magunguna bayan an kona wasu sansanonin 'yan bindigan da ke Udawa a Chikun.

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

Gwamnatin Kaduna ta fallasa hanyoyi 6 da 'yan bindiga ke samun kudin shiga

A wani labari na daban, Gwamnatin jihar Kaduna ta fallasa inda miyagun 'yan bindiga da suka addabi jihar ke samun kudaden shiga.

Daga cikin hanyoyin samun kudinsu kamar yadda gwamnatin jihar tace, shi ne wurin karbar kudin fansa daga 'yan uwan wadanda suka sace, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a rahoton tsaro na watanni uku da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya mika wa gwamnatin jihar kuma Daily Trust ta samu kwafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel