Gwamnatin Kaduna ta fallasa hanyoyi 6 da 'yan bindiga ke samun kudin shiga

Gwamnatin Kaduna ta fallasa hanyoyi 6 da 'yan bindiga ke samun kudin shiga

  • Gwamnatin Kaduna ta ce 'yan bindiga na samun kudin shiga ta hanyar karbar kudin fansa daga 'yan uwan wadanda suka sace
  • Sauran hanyoyin samun kudin shigan sun hada da siyar da shanun sata, cinikayyar makamai, bayar da hayar makamai da sauransu
  • Sai dai su kan kashe kudaden wurin magani, shaye-shaye, biyan masu kai musu bayanan sirri da sauran munanan hanyoyi

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta fallasa inda miyagun 'yan bindiga da suka addabi jihar ke samun kudaden shiga.

Daga cikin hanyoyin samun kudinsu kamar yadda gwamnatin jihar tace, shi ne wurin karbar kudin fansa daga 'yan uwan wadanda suka sace, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a rahoton tsaro na watanni uku da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya mika wa gwamnatin jihar kuma Daily Trust ta samu kwafi.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

Gwamnatin Kaduna ta fallasa inda 'yan bindiga ke samun kudin makamai
Gwamnatin Kaduna ta fallasa inda 'yan bindiga ke samun kudin makamai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoton ya lissafo sauran hanyoyin da kudi ke shigo musu da suka hada da siyar da dabbobin sata, ribar cinikayyar makamai da kuma bayar da hayar makamai ga wasu kungiyoyin ta'addanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bangaren rahoton ya ce: "Wasu kungiyoyi na bayar da hayar makamai ga kungiyoyin da basu da shi kuma su raba kudin da suka samu wurin ta'addanci."

Sauran hanyoyin samun kudin sun hada da harajin dole da suke kallafa wa manoma a kan gonakinsu.

Rahoton ya kara da bayyana cewa, su kan bai wa masu kai musu bayanan sirri jari domin kasuwanci wanda suke aike musu da ribar.

Ya kara da bayyana yadda 'yan bindigan ke kashe kudin ta hanyar siyan bindigogi, makamai da abinci.

Sauran sun hada da kudaden kaiwa da kawowa, magani, siyan kayan shaye-shaye, biyan masu kai musu bayanan sirri, karfafa kasuwanci wanda masu kai musu bayanai ke yi da kuma kai wa bokaye kudi domin nasarar ayyukansu.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Yadda 'yan bindiga suka yi wa jama'a kisan kiyashi a kasuwar Sokoto

Ku tattauna da Igboho, IPOB kamar yadda na ke yi da 'yan bindiga, Gumi ga malaman kudu

A wani labari na daban, Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci malaman kudancin kasar nan da su tashi tsaye wurin tattaunawa da masu tada kayar baya tare da assasa rashin tsaro a yankunansu kamar yadda ya ke wa 'yan bindiga.

Fitaccen malamin ya sanar da hakan ne yayin da ya ke fitar da takarda kan martaninsa ga masu bukatar gwamnatin tarayya ta ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda, Daily Trust ta ruwaito.

A makon da ya gabata, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya sake bukatar gwamnatin tarayya da ta bayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel