Sojoji sun halaka 'yan bindiga yayin da "dogarin Biafra" suka kai musu farmaki a Abia

Sojoji sun halaka 'yan bindiga yayin da "dogarin Biafra" suka kai musu farmaki a Abia

  • Sojojin Najeriya da ke jihar Abia sun halaka dogarin kasar Biafra a jihar bayan sun kai musu farmaki
  • Dogaran Biafra dauke da miyagun makamai sun bayyana a motoci sannan suka fada wa sojin Najeriya
  • Babu kakkautawa zakakuran dakarun suka bude musu wuta inda wasu suka tsere da raunika sannan 1 ya mutu

Ohafia, Abia - Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun ta na rundunar atisayen Golden Dawn sun halaka dogaran kasar Biafra a yankin kudu maso gabas na Najeriya.

Mamacin ya na daya daga cikin 'yan bindigan da suka kai farmaki inda dakarun su ke a Amaekpu da ke karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia.

The Cable ta ruwaito cewa, Onyema Nwachukwu, daraktan hulda da jama'a na rundunar ne ya sanar da wannan cigaban a wata takarda da ya fitar a Abuja ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An tsinci gawar jami'in kwastam da miyagu suka yi garkuwa da shi

Nwachukwu ya ce dogaran sun bayyana dauke da miyagun makamai kuma cike da ababen hawa sannan suka bude wa dakarun wuta amma jajircewa ta sa aka ga bayansu.

Sojoji sun halaka 'yan bindiga yayin da "dogaran Biafra" suka kai musu farmaki a Abia
Sojoji sun halaka 'yan bindiga yayin da "dogaran Biafra" suka kai musu farmaki a Abia. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya ce 'yan bindigan sun bar ababen hawansu kuma suka tsere da miyagun raunikan da suka samu sakamakon harbi kuma suka bar gawar dayan da aka kashe.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, mai magana da yawun rundunar ya ce sojoji sun samu wata bindiga mai hatsari tare da sauran makamai.

"Yayin da 'yan ta'addan suka tsere ganin an fi karfinsu, dakarun da ke aiki a sansanin Ohaozara da ke jihar Ebonyi sun tare su," yace.
"Sojojin sun kara samun wasu motoci uku yayin da suka damke dan bindiga daya," ya kara da cewa.

Take hakkin dan Adam: UN ta aiko wa Najeriya wasika, ta bukaci bayanai 5 game da Kanu

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

A wani labari na daban, majalisar dinkin duniya ta bukaci gwamnatiin tarayya da ta samar da wasu bayanai kan shugaban kungiyar 'yan awaren IPOB, Mazi Nnamdi Kanu.

Jerin tambayoyin suna kunshe ne a wata takarda da majalisar dinkin duniyan ta aiko wa da gwamnatin tarayya mai kwanan wata 27 ga watan Augusta.

Kamar yadda majalisar dinkin duniyan ta ce, ta samu rahotanni kan zargin take hakkin dan Adam da gwamnatin tarayya ke wa Kanu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel