Gwamna Ganduje ya gabatar da N196.3bn a matsayin kasafin kudin shekarar 2022

Gwamna Ganduje ya gabatar da N196.3bn a matsayin kasafin kudin shekarar 2022

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya gabatar da naira biliyan 196.3 a matsayin kasafin kudin 2022
  • A kasafin kudin, an ware ma bangaren ilimi kaso mai tsoka na naira biliyan 51.6, wanda ke wakiltan kaso 26 cikin 100
  • Ganduje ya gabatar da kasafin kudin ne a yau Alhamis, 28 ga watan Oktoba, a zauren majalisar dokokin jihar

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya gabatar da naira biliyan 196.3 a matsayin kasafin kudin 2022.

Gwamnan ya gabatar da kasafin kudin ne a gaban majalisar dokokin jihar a ranar Alhamis, 28 ga watan Oktoba, Daily Trust ta rahoto.

Gwamna Ganduje ya gabatar da N196.3bn a matsayin kasafin kudin shekarar 2022
Gwamna Ganduje ya gabatar da N196.3bn a matsayin kasafin kudin shekarar 2022 Hoto: TVC News
Asali: UGC

A kasafin kudin, bangaren ilimi ya samu kaso mai tsoka na naira biliyan 51.6, wanda ke wakiltan kaso 26 cikin 100, TVC News ta rahoto.

Kara karanta wannan

CBN ta magantu kan dalilin bacewar manhajar e-Naira a intanet, yaushe kuma za ta dawo

Ma’aikatar lafiya kuma ta samu naira biliyan 15 sannan naira biliyan 33 zai tafi kan ayyuka da ababen more rayuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da jimillar kudaden shigar da aka gabatar a kan naira biliyan 146.8, gwamnan ya gabatar da naira biliyan 33 a matsayin kudaden shiga na cikin gida (IGR) da kuma naira biliyan 37 a matsayin kudaden shiga daga harajin kayayyaki (VAT).

Gwamna Ganduje ya ce yayin da jimillar kudin kasafin ya kama naira biliyan 196.3, manyan kudaden da za a kashe zai kama naira biliyan 107.8 inda kudaden da za a kashe na yau da kullun ya kama naira biliyan 88.4.

Kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya bayar da tabbacin cewa majalisar za ta gaggauta shiga aiki don aiwatar da kasafin kafin karshen 2021 ba tare da tangarda ba.

Ya yi tsokaci a kan illar karancin kudaden shiga, musamman wajen rage IGR, inda ya bayyana cewa matsalar ta fi shafar Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha

Chidari ya bukaci hukumar kudaden shiga ta jihar da ta duba hanyoyin samar da karin kudade da toshe duk wata kafa a wajen tattara kudade a jihar maimakon dogaro kan kudaden shiga daga ma’aikatar mai mara tabbas.

Ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa wa manoma domin tabbatar da tsaron abinci sakamakon rashin isasshen ruwan sama a shekarar wanda ya lalata albarkatun gona da dama.

Shugaba Buhari ya ware kusan Naira biliyan 20 domin kirkirar manhajoji a shekarar 2022

A wani labarin, Gwamnatin Najeriya za ta kashe Naira biliyan 19 domin kirkirar manhajojin komfuta a shekarar 2020. Premium Times ce ta fitar da wannan rahoton.

Kasafin kudin da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar wa ‘yan majalisa ya nuna akwai Naira biliyan 19 da za a batar a kan manhajojin.

An kacancana kudi tsakanin ofisoshi kusan 200 na ma’aikatun tarayya. Akwai yiwuwar kudin ya zarce haka saboda ba a tattara duka hukumomin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar Lafiya na shirin karban bashin N82bn don sayen ragar kariya daga cizon sauro

Asali: Legit.ng

Online view pixel