Shugaba Buhari ya ware kusan Naira biliyan 20 domin kirkirar manhajoji a shekarar 2022

Shugaba Buhari ya ware kusan Naira biliyan 20 domin kirkirar manhajoji a shekarar 2022

  • Gwamnatin Tarayya za ta batar da makudan biliyoyi a kan kirkirar manhajoji
  • An ware wa ma’aikatu da wasu cibiyoyin gwamnati sama da N19b da wannan nufi
  • Kasashen Duniya za su kashe makudan biliyoyi a kan na’urorin zamani a 2022

Abuja - Gwamnatin Najeriya za ta kashe Naira biliyan 19 domin kirkirar manhajojin komfuta a shekarar 2020. Premium Times ce ta fitar da wannan rahoton.

Kasafin kudin da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar wa ‘yan majalisa ya nuna akwai Naira biliyan 19 da za a batar a kan manhajojin.

An kacancana kudi tsakanin ofisoshi kusan 200 na ma’aikatun tarayya. Akwai yiwuwar kudin ya zarce haka saboda ba a tattara duka hukumomin gwamnati ba.

Nuku-nuku a kasafin kudin Najeriya

Akwai wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ba a san abin da kasafin kudinsu ya kunsa ba.

Read also

Kasafin kudin Buhari: Za a sayi janareta na N104bn, aikin wutar Mambila kuma N650m

Daga cikin cibiyoyin da kundin kasafin kudin su yake a boye akwai babban bankin kasa na CBN, hukumar kwastam da NNPC, da FIRS mai tattara haraji na kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Punch ta ce hukumar FIRS za ta batar da Naira biliyan 2.04 a kan na’urorin komfuta. Haka zalika hukumar za ta kashe wasu Naira biliyan 1.3 kan kayan na’urorin.

Shugaba Buhari
Buhari ya gabatar da kasafin kudi Hoto: www.naijanews.com
Source: UGC

Kudin sayen manhajoji ya karu a 2022

A dalilin tulin kudin da za a batar wajen saye ko kirkirar manhajoji, bashin da Muhammadu Buhari zai ci a shekara mai zuwa ya kai Naira tiriliyan shida.

Masana tattali suna hasashen cewa Kasashen Duniya za su kashe kudi masu yawa a shekara mai zuwa yayin da ake farfado wa daga annobar cutar COVID-19.

Ana sa rai kudin da za a batar wajen sayen komfuta da kayan na’urorin za su kai Dala biliyan 550. Hakan ya nuna an samu karin akalla 6.5% daga shekarar 2021.

Read also

Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba

A shekarar 2020 gwamnatin Kogi tace ta kashe N150m kan manhajar COVID-19. Wani gwamna ya taba cewa ya kashe N78m wajen gina shafinsa na yanar gizo.

Rokon Gwamnan Kaduna

Dazu aka ji gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya rubuta wasika, yana so a ayyana ‘Yan bindigan Arewa a matsayin ‘yan ta’adda ko a ce masu tada kafar baya.

Gwamnan jihar Kaduna ya goyi bayan masu so a kira ‘Yan bindiga da masu tada-tsaye.

Source: Legit

Online view pixel