CBN ta magantu kan dalilin bacewar manhajar e-Naira a intanet, yaushe kuma za ta dawo

CBN ta magantu kan dalilin bacewar manhajar e-Naira a intanet, yaushe kuma za ta dawo

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya magantu kan dalilin da yasa manhajar e-Naira ya bace a kafar Play Store
  • A baya an ruwaito cewa, manhajar ta bace kwanaki kadan bayan kaddamar da ita da shugaba Buhari ya yi
  • A halin yanzu, babban bankin ya bayyana cewa, watakila manhajar ta dawo aiki a yau bayan kammala gyara

Ebonyi - The Nation ta ruwaito cewa, Babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana dalilin bacewar sabuwar jakar kudin intanet mallakar Najeriya wato e-Naira da aka kaddamar ba shiri daga kafar Play store na kamfanin Google.

Bankin ya bayyana cewa bacewar manhajar na wucin gadi ne kawai saboda yana fuskantar wani muhimmin ingantayya da nufin magance matsalolin da aka samu tun lokacin kaddamar da shi.

Daraktan Sadarwa na Bankin, Osita Nwanisobi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 28 ga watan Oktoba a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Wata Jiha a Najeriya Ya Rasu

Da dumi-dumi: CBN ta magantu kan dadin da yasa ta cire manhajar eNaira a intanet
Buhari yayin kaddamar manhajar e-Naira | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Ya yi wannan jawabi ne a wani bikin baje koli na CBN na shiyyar siyasar yankin kudu maso gabas, wanda kuma aka gudanar lokaci guda a jihohin Ebonyi da Abia.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Punch ta ruwaito a baya cewa, manhajar ta e-Naira Speed Wallet ta bace daga kafar Play Store na kamfanin kwanaki kadan bayan kaddamar da shi a ranar Litinin, 25 ga Oktoba, 2021.

Manhajar ta samu sama da saukewa 200,000 cikin sa'o'i 24 kafin ta bace bat, lamarin da ke nuni da yawan masu sha'awar kudaden intanet na Babban Bankin.

Wani bincike mai sauri da aka yi a Google Play Store ya nuna babu manhajar e-Naira Speed Wallet amma har yanzu manhajar eNaira Speed Merchant tana nan don saukewa akan wayoyin android.

Nwanisobi ya ce ana sa ran manhajar za ta dawo yau bayan sabuntata.

Kara karanta wannan

Cin Bashi Don Gudanar Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN

Ya ba da tabbacin cewa manhajar tana da tsaro sosai saboda ta dogara da fasahar tantance bayanai kafin amfani da ita.

Ya ce ‘yan Najeriya ta wani bangare suna da hannu wajen haddasa kura-kuran da aka samu wanda ya ce sun taimaka wajen bacewar ta daga kafar.

A cewarsa, gazawar da ‘yan Najeriya da yawa suka yi wajen shigar da bayanansu daidai lokacin da suke yin rajista a manhajar ya taimaka wajen samun matsala.

Kwana 2 bayan kaddamar da e-Naira, masu Andriod na kuka yayinda manhajar ta samu matsala a Google Store

A wani labarin, Manhajar eNaira ya yi batan dabo daga kan Google Play Store kimanin kwanaki biyu bayan kaddamar da ita, rahoton Punch ya nuna haka.

Wannan ya faru ne bayan sama da mutum 100,000 masu amfani da waya kalar Android sun saukar da manhajar don amfani.

Amma ga masu wayar iPhone, manhajar har yanzu tana nan kuma ana cigaba da amfani da ita.

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a

Asali: Legit.ng

Online view pixel