Daga karshe, shugaba Buhari ya gano dalilai uku da suka jawo tabarbarewar tsaro

Daga karshe, shugaba Buhari ya gano dalilai uku da suka jawo tabarbarewar tsaro

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa matsalar tsaro ta addabi Najeriya
  • Ya kuma nemi hadin gwiwar kasashen makwabta wajen kokarin yaki da ta'addanci da ake yi a kasar
  • Shugaban ya kuma bayyana dalilai guda uku da suke jawo kara hauhawar matsalolin tsaro a Najeriya

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya ce abubuwa daban-daban ne suka jawo matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

Ya yi wannan jawabi ne a wani takaitaccen biki da aka yi a fadar gwamnati da ke Abuja, inda Jakadun Japan, Tarayyar Turai, Burundi, Denmark, Finland, Ireland, Cape Verde, Faransa, Qatar; da manyan kwamishinonin kasar Saliyo da Ghana suka karbi wasikun amincewa.

Ya ce ana bukatar karin hadin gwiwa domin shawo kan kalubalen rashin tsaro a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Read also

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

Dalilin da yasa muke fuskantar kalubalen tsaro - Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Ya ce:

“A matsayinmu na gwamnati da kuma kasa baki daya, muna ci gaba da samun ci gaba mai dorewa duk da kalubalen da ake fuskanta musamman a fannin tsaro.

Da yake bayyana dalilin farko na matsalar tsaro da ya addabi kasar, Buhari ya ce:

“Abubuwa daban-daban ne suka haifar da hakan, daga cikinsu akwai, na farko, rashin tsaro da ke da nasaba da ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane, laifuffukan yanar gizo, da kuma batutuwan da suka shafi teku, ayyuka ne na kan iyaka da suka wuce karfin kowace kasa guda don shawo kan su yadda ya kamata.
‘’Saboda haka, al’amuran tsaro sun zama aikin duk kasashen duniya, su hada kai domin shawo kan lamarin.

Bangare na biyu shugaban ya bayyana cewa, iyakokin Najeriya suna da girma, wannan yasa kula da shigo da abubuwa ke da matukar wahala.

Read also

Da duminsa: Bayan harin yan ta'adda, jirgin kasan Abuja/Kaduna zai koma aiki ranar Asabar

A kalamansa:

“Na biyu, iyakokinmu suna da tsayi sosai kuma suna da fadi, kuma ingantaccen aikin tsare su ya zama kalubale mai ban tsoro.

A bangare na uku, shugaban ya ce:

"Na uku, saukin yaduwar kananan makamai, daga yankin Sahel-Libya da kuma yankin Afirka ta Tsakiya, sun ba da damar samun damar yin amfani da wadannan makamai a cikin sauki wanda ke tattare da tsaron kasa da na yanki."

Sai dai ya ce duk da wadannan manyan kalubalen, kokarin da gwamnatinsa da rundunar sojin kasar suka yi ya haifar da “tasiri wajen rage karfin ‘yan ta’adda a fadin kasar nan.”

A halin da ake ciki, yankuna da yawa a Najeriya na fuskantar kalubalen tsaro, lamarin da ya kai ga kashe-kashen rayuka da yawa a kasar.

Yankin Arewa shine yankin da yafi fuskantar kalubalen tsaro daga hare-haren 'yan bindiga zuwa na 'yan Boko Haram da ISWAP.

Read also

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

Firaministan Burtaniya, Boris Johnson, ya ce kasarsa a shirye take domin taimakawa Najeriya wajen yaki da matsalolin rashin tsaro da suka addabi kasar, BBC ta ruwaito.

ISWAP ta hallaka wasu jiga-jigan kwamandojin Boko Haram da mabiyansu 18

A wani labarin, jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa an kashe manyan jiga-jigan kungiyar Boko Haram guda biyu, Amir Modou Marte da Amir Moustapha Baga .

An kawar da su ne a wani kwanton bauna da mayakan abokan hamayyarsu na ISWAP suka yi a ranar Lahadi 24 ga watan Oktoba.

An tattaro cewa wasu 'yan ta'adda 15 na daga cikin wadanda kungiyar Boko Haram ta kashe a lokacin kwanton baunar da suka yi a Toumboun Gadura'a.

Source: Legit.ng

Online view pixel