Najeriya ta zo karshe: Martanin jama'a kan yunkurin China na bude banki a Najeriya

Najeriya ta zo karshe: Martanin jama'a kan yunkurin China na bude banki a Najeriya

Sanarwar da jakadan kasar China a Najeriya Mista Cui Jianchun ya yi na cewa 'yan Najeriya su sa ran bankunan kasar China za su fara aiki a kasar, ya haifar da martani daban-daban daga 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta.

Yayin da wasu ‘yan Najeriya ke ganin hakan a matsayin abin farin ciki, wasu kuma na cewa abin kunya ne kuma abin kaico ga al’ummar kasar.

SaharaReporters ta ruwaito cewa, jakadan na China ya bayyana, dama akwai yarjejeniya kan wannan yunkuri tsakanin Najeriya da China.

Bankin China zai fara aiki a Najeriya
China ta yanke shawarar bude bankuna a Najeriya | Hoto: thediplomat.com
Asali: UGC

Charles Chima

"Duk da cewa, kasuwanci ya dogara da matakin ilimin mutum. Mafi yawan lokuta, idan ba ka da isasshen ilimi ko kuma kana cikin matsi, wani zai iya wuce ka. Kuma idan aka yi haka, sakamakon zai nuna mafi kyau. Matsi a cikin al'ummar Afirka sun yi yawa!"

Kara karanta wannan

Kasar Sin zata bude bankuna a Najeriya, wannan shine yarjejeniyar da mukayi: Jakadan Beijing

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Felix Williams

"Najeriya ta kade, nan ba da jimawa ba za su fara gina ofisoshin 'yan sanda na kasar China. BRI na kasar China ya fara aiki tukuru."

Musa Yusuf

"Abin takaici ne, gwamnatin Najeriya ta shuka irin barnar ta kanta, ta hanyar ba wa wadancan mutanen kasar China damar kafa Bankinsu a Najeriya. Irin wadannan mutane sun kwace kasuwar masaku a Kano da Najeriya baki daya, yanzu kuma bangaren banki."

Venatius Mmeka

“Abin farin ciki ne, dalilin da ya sa akasarin kayayyakin yau da kullum da muke amfani da su daga kasar China suke, zai rage tsada, ba za mu kara bukatar dala don sayen kayayyaki daga kasar China, Naira da Yuan, za a samu tsayayyen farashi. Dala ba za ta kara haurar da hajojinmu ba, don haka muna maraba da ra'ayin aikin bankin kasar China a Najeriya."

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Buhari zai ba masu digiri bashin miliyoyi saboda rage zaman banza

Ibrahim Iro Wudil

"Yanzu duk abubuwan da muke bukata domin magance rashin aikin yi an rasa meh za'a kawo mana sai banki bayan duk wanda muke dasu a kasar nan."

Zwalatha Daniel Lambo

"Abun yakusa ya faru da najeriya. Sun bamu bashi, dole su bude bankuna a najeriya domin sune nan gaba zasu soma karban haraji na kasa gabadaya. Nigeria is sold already."

Kasar China zata bude bankuna a Najeriya, wannan shine yarjejeniyar da mukayi: Jakadan Beijing

A tun farko, Jakadan kasar China dake Najeriya, Mr Cui Jianchun, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin kasarsa zata budewa bankuna a Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa hakazalika za'a iya bude bankunan Najeriya a China, inda yace wannan na cikin abubuwan da suka wajaba ayi don tabbatar da yarjejeniyar canjin kudi tsakanin Najeriya da China ta yiwu.

Jakadan China, ya ce yanzu haka yana aiki tukuru don ganin cewa bankuna kasarsa su fara aiki a Najeriya, hakazalika na Najeriya a kasar China.

Kara karanta wannan

2023: 'Ku sani babu rumfar zabe a kafafen sada zumunta' - YPP ta shawarci matasan Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel