Bayan kwanaki 50: Tsohon sanata na tsare a hannun ‘yan bindigar da suka sace shi

Bayan kwanaki 50: Tsohon sanata na tsare a hannun ‘yan bindigar da suka sace shi

  • Har yanzu 'yan bindigar da suka yi garkuwa da tsohon sanatan da ya wakilci yankin Akwa Ibom ta kudu, Nelson Effiong, sun ki sakin shi
  • Zuwa yanzu, Mista Effiong ya shafe sama da kwanaki 50 a hannun wadanda suka sace shi
  • Sanata Shehu Sani, wanda ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya ya nuna damuwarsa a kan haka

Jihar Akwa Ibom - Tsohon sanata daga jihar Akwa Ibom, Nelson Effiong, ya shafe tsawon kwanaki 50 a tsare, tun bayan da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi a ranar 6 ga watan Satumba a Uyo.

Antai Effiong, wani lauya kuma kanin tsohon sanatan, a ranar Laraba, 27 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa har yanzu wadanda suka yi garkuwa da shi basu sake sa ba, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun saki ‘yan asalin jihar Benue da suka sace a Zamfara

Bayan kwanaki 50: Tsohon sanata na tsare a hannun ‘yan bindigar da suka sace shi
Bayan kwanaki 50: Tsohon sanata na tsare a hannun ‘yan bindigar da suka sace shi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce:

"Ba a saki tsohon sanatan ba, da ace an sake shi, da iyalan sun yi magana zuwa yanzu."

Mista Effiong ya ce iyalan na ta tattaunawa da tsohon sanatan, amma ya ki yin karin bayani kan lamarin a lokacin da aka tambaye shi ko wadanda suka sace shi sun nemi a biya kudin fansa.

Hakazalika, Shehu Sani, tsohon sanata daga jihar Kaduna, ya je shafinsa na Facebook a ranar Talata domin nuna damuwa kan rashin sakin tsohon takwaran nasa.

Ya rubuta a shafin nasa bayan wallafa hotunansu tare cewa:

"Sanata Effiong (a bayana) ya shafe sama da kwanaki 50 a hannun masu garkuwa da mutane. Addu'ana na tare da shi da iyalinsa."

An tattaro cewa wasu 'yan bindiga cikin motar Toyoya Camry ne suka sace Mista Effiong.

Kara karanta wannan

Labari da ɗuminsa: An bindige wani mutum har lahira a Imo

Tsohon sanatan ya wakilci yankin Akwa Ibom ta kudu daga 2015 zuwa 2019. Kafin nan, ya yi aiki a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Akwa Ibom. Ya kuma kasance jigon APC.

'Yan bindiga sun kai farmaki gidan tsohon gwamna, sun yi garkuwa da kanin matarsa

A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa ‘Yan bindiga sun kai farmaki Talata Marafa, mahaifar tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, sannan suka yi awon gaba da wani surukinsa.

Maharan sun kai hari garin ne a yammacin ranar Litinin, inda suka yi garkuwa da surukin tsohon gwamnan da kuma matar makwabcinsa, Sahara Reporters ta ruwaito.

Rahoton ya nuna cewa wannan shinro ne karo na farko da ake kai hari hedkwatar karamar hukumar Talata Marafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel