'Yan bindiga sun kai farmaki gidan tsohon gwamna, sun yi garkuwa da kanin matarsa

'Yan bindiga sun kai farmaki gidan tsohon gwamna, sun yi garkuwa da kanin matarsa

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari
  • Maharan sun kuma yi garkuwa da kanin matar Yari mai suna Hussain da kuma matar makwabcinsa
  • Sun kai harin ne a kan babura da misalin karfe 11:30 na dare sannan suka yi ta harbi ba kakkautawa don tsorata jama'a

Zamfara - ‘Yan bindiga sun kai farmaki Talata Marafa, mahaifar tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, sannan suka yi awon gaba da wani surukinsa.

Maharan sun kai hari garin ne a yammacin ranar Litinin, inda suka yi garkuwa da surukin tsohon gwamnan da kuma matar makwabcinsa, Sahara Reporters ta ruwaito.

'Yan bindiga sun kai farmaki gidan tsohon gwamna, sun yi garkuwa da kanin matarsa
'Yan bindiga sun kai farmaki gidan tsohon gwamna, sun yi garkuwa da kanin matarsa Hoto: The Guardian
Asali: Depositphotos

Rahoton ya nuna cewa wannan shinro ne karo na farko da ake kai hari hedkwatar karamar hukumar Talata Marafa.

Karamar hukumar ta fuskanci hare-hare a baya, kamar su garkuwa da dalibai sama da 300 a makarantar sakandaren mata ta gwamnati, Jangebe, amma duk a kauyuka suka faru.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya hannun yan daba a majalisar dokokin jihar Zamfara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani hadimin Yari, Bello Ruwan Bado, ya tabbatar da sace Auwal Hussain wanda aka fi sani da Sarki.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Hussain, wanda ya kasance kanin uwargidar Yari, yana zaune ne a gidan tsohon gwamnan kafin yayi aure kuma an ce yana daya daga cikin makusantan Yari.

Hakazalika maharani sun kuma yi garkuwa da matar makwabcin Hussain, Surajo.

Wani makwabcinsa mai suna Mustapha Lawan, ya ce ya ji karar harbi da muryoyin ‘yan bindigar.

Ya ce:

“Mun ji lokacin da ‘yan bindigar suka zo da daddare. Sun zo ne a kan Babura sannan suna ta harbi a sama domin tsorata mutane. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare.
“Tun da har ‘yan bindigar za su iya shigowa yankin nan da ake ganin ya fi kowanne tsaro a Talata Marafa, wacce ta kuma kasance gari na biyu a mafi girma a jihar, toh lallai abun tsoro ne. sun shafe sama da awa daya ba tare da jami’an tsaro sun zo don kalubalantarsu ba.”

Kara karanta wannan

Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa

Wani abokin Hussain, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce suna ganin akwai hannun ‘yan kwarmato a lamarin.

Ya ce:

“Kwanan nan Sarki ya dawo daga Dubai, kuma a lokacin da ‘yan bindigar suka zo, sun ma tambaye shi ko ya kawo wani abu daga Dubai. Kuma basu yi garkuwa da kowa ba baya ga matar makwabcin sarki.”

Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya hannun yan daba a majalisar dokokin jihar Zamfara

A wani labarin kuma, mamban majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltan Arewacin Talata-Mafara, Hanarabul Shamsudden Hassan, ya tsallake rijiya da baya ranar Alhamis a zauren majalisar.

Wannan abu ya auku ne yayin taron tantance mutum biyu da gwamnan jihar ya gabatar da sunayensu don tabbatar da su matsayin kwamishanoni a gwamnatinsa, rahoton Punch.

Dan majalisan ya nuna rashin goyon bayansa kan daya daga cikin wadanda gwamnan ya turo sunayensu, Hajiya Rabi Ibrahim Shinkafi, wacce ta rike mukamin mai baiwa gwamna Matawalle shawara.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

Asali: Legit.ng

Online view pixel