Labari da duminsa: An bindige wani mutum har lahira a Imo

Labari da duminsa: An bindige wani mutum har lahira a Imo

  • Wasu bata gari da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun bindige wani mutum har Lahira a Imo
  • Rahotanni sun bayyana cewa ya tafi Okwelle ne domin yin siyaya suka gan shi a hanya suka gane dan banga ne
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abattam ya tabbatar da afkuwar lamarin

Jihar Imo - Daily Trust ta rahoto cewa an bindige wani mutum har lahira a Abba a karamar hukumar Nwangele na jihar Imo.

Rahoton ya ce wasu bata gari ne suka bindige mutumin mai suna Fidelis Nnadi a kan hanyar Okwelle zuwa Umuezealaibe.

Labari da duminsa: An bindige wani mutum har lahira a Imo
An bindige wani mutum har lahira a Imo. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan sanda sun samo gawar basaraken da aka yi garkuwa da shi

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutumin da aka kashe dan banga ne.

An ce ya bar kauyensu ta Oguwuaga zuwa Okwelle don ya siyo wasu kayayyaki yana kan hanyarsa na dawowa ne yan daban suka tare shi.

Yan daban da aka ce sun sace wata mata da jinjirinta sun gane cewa shi jami'an tsaro ne hakan yasa suka bindige shi suka tsere.

Wata majiya a garin ya ce:

"Na yi magana da kwamandan yan bangan kuma ya ce Okwele ya tafi yin siyayya ne abin ya faru da shi.
"Masu garkuwar suna hanyar zuwa Okigwe ne suka hangi shi suka gane shi jami'in tsaro ne suka bindige shi. An ce ya fito ne daga Ogwuaga."

'Yan sanda sun tabbatar da afkuwar lamarin

Mai magana da yawun yan sanda na jihar Imo, CSP Mike Abattam ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce yan sanda sun fara bincike.

Ana ta zargin haramtaciyyar kungiyar IPOB ta kai hare-hare a yankin na kudu amma ta musanta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

A satin da ta gabata duk dai a Imo, an halaka wasu sarakuna uku a wurin taro.

An kuma cinna wa fadar wani sarkin wuta bayan ya tsere.

A ranar Lahadi, an bindige yan sanda uku a caji ofis da ke Ebonyi.

Jami'an tsaro na kokarin kawo karshen hare-haren amma har yanzu abin ya ci tura.

Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun saki wadanda aka tsare sun kona motocin sintiri

A wani rahoton, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Litinin, sun kai hari hedkwatar yan sanda da ke karamar hukumar Ohaukwu da ke jihar Ebonyi.

A ruwayar SaharaReporters, 'yan bindigan sun kai harin ne misalin karfe 2 na dare inda suka saki dukkan wadanda ake tsare da su a ofishin yan sandan.

Maharan sun kuma kona wasu motoccin sintirin yan sanda sannan wasu jami'an yan sandan sun tsere da raunin bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel