Secondus bai yi mana adalci ba idan ya rusa PDP, Shugaban kwamitin dattawan jam'iyyar Walid Jibrin

Secondus bai yi mana adalci ba idan ya rusa PDP, Shugaban kwamitin dattawan jam'iyyar Walid Jibrin

  • Manyan dattawan PDP na kira ga Uche Secondus yayi hakuri ya janye karar da ya shigar kotu kan jam'iyyar
  • Uche Secondus wanda aka fitittika daga kujerarsa ya lashi takobin ganin cewa taron gangamin da za'a gudanar karshen watan nan bai yiwu ba
  • Jam'iyyar PDP ta baiwa Arewacin Najeriya damar gabatar da shugaban jam'iyya na kasa

Abuja - Shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Walid Jibril, ya yi kira ga dakataccen shugaban jam'iyyar Walid Jibrin kada ya kawo hargitsi cikin jam'iyyar.

Alhaji Walid ya bayyana hakan ne yayin jawabi a shirin Sunrise Daily, na ChannelsTV ranar Laraba, TheCable ta bibiya.

A cewarsa, uwar jam'iyyar ta yanke shawara ta karshe kuma lallai za'ayi taron gangami ranar da aka shirya.

Kara karanta wannan

Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki

Yace ba zai kyautatu ga Secondus, wanda yana cikin iyayen jam'iyyar PDP ya damula musu lissafi ba.

A cewarsa:

"Secondus mamban kwamitin amintattu ne, ya zama shugaban uwar jam'iyya gaba daya, shin yanzu ne zai yi fito-na-fito na shawarar da jam'iyyar ta yanke? Gaskiya bai kyauta ba idan yayi haka."
"Komai fa zai zo karshe. Ya kasance cikin jam'iyyar nan tun lokacin da aka kafata. Zai mutu ne?"
"Ina mai bayyana cewa za'a yi taron gangami kamar yadda aka shirya ranar 30 ga watan nan kuma zamu halarta don gudanar da ayyukanmu don cigabar jam'iyyarmu."

Secondus bai yi mana adalci ba idan ya rusa PDP, Shugaban kwamitin dattawan jam'iyyar Walid Jibrin
Secondus bai yi mana adalci ba idan ya rusa PDP, Shugaban kwamitin dattawan jam'iyyar Walid Jibrin
Asali: UGC

Kotu ta sanya ranar sauraran karar da Uche Secondus ya shigar kan PDP

Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a garin Fatakwal, jihar Ribas ta sanya ranar Alhamis 28 ga watan Oktoba domin sauraran karar da tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Prince Uche Secondus ya shigar kan batun dakatar dashi.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Shugaban APC Buni da tawagarsa sun ziyarci Tinubu a gidansa

Secondus a cikin daukaka kara mai lamba CA/PH/ 339, yana rokon kotu da ta hana jam’iyyar PDP gudanar da taronta na gangami na kasa wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 30 da 31 ga Oktoba, 2021, Punch ta ruwaito.

Rashin tabbas a PDP, kila a fasa gudanar da zabukan sababbin shugabannin jam’iyya

Akwai kalubale a jam’iyyar PDP a game da zaben shugabanni na kasa da za ayi ranar Asabar, saboda yiwuwar kotu ta dakatar da shirya gangamin.

Hakan ya bayu ne ga kafewar Prince Uche Secondus wanda ya ki janye karar da ya shigar a kotu, yana kalubalantar sauke shi da aka yi kafin cikar wa’adinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel