Rikicin PDP: Kotu ta sanya ranar sauraran karar da Uche Secondus ya shigar kan PDP

Rikicin PDP: Kotu ta sanya ranar sauraran karar da Uche Secondus ya shigar kan PDP

  • Uche Secondus, tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya maka jam'iyyar a kotu kan dakatar dashi
  • Kotu a baya ta yanke hukuncin dakatar da Uche Secondus a matsayin shugaban jam'iyyar ta PDP
  • An sanya ranar 28 ga watan Oktoba domin sauraran sabuwar karar da Secondus ya shigar kan PDP

Ribas - Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a garin Fatakwal, jihar Ribas ta sanya ranar Alhamis 28 ga watan Oktoba domin sauraran karar da tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Prince Uche Secondus ya shigar kan batun dakatar dashi.

Secondus a cikin daukaka kara mai lamba CA/PH/ 339, yana rokon kotu da ta hana jam’iyyar PDP gudanar da taronta na gangami na kasa wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 30 da 31 ga Oktoba, 2021, Punch ta ruwaito.

Da dumi-dumi: Kotu za ta yanke yaushe za a yi taron gangamin PDP
Korarren shugaban jam'iyyar PDP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hakazalika, inji rahoton This Day, kotun daukaka karar ta baiwa lauyoyin PDP awanni 24 su gabatar da martaninsu.

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan Boko Haram sun yi dira garin Katarko a jihar Yobe yau Asabar

A ranar 23 ga watan Agusta, wasu ‘yan jam’iyyar sun shigar da kara mai lamba PHC/2183/CS/2021 a babbar kotun jihar Ribas, sashin shari’a na Fatakwal, tare da Secondus da PDP a matsayin wadanda ake kara.

A ranar 10 ga Satumba, 2021, kotu ta yanke hukunci, ta kuma hana Secondus gudanar da ayyukan shugaban jam'iyyar PDP na kasa.

Rikicin PDP na kara kamari yayin da ta hana wasu fitattun mambobi 3 tsayawa takara

A wani labarin, Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kwamitin tantancewa na jam'iyyar PDP ya hana 'yan takara uku tsayawa takarar mukamai a kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar.

Wadanda ba su cancanta ba da mukaman inji PDP sun hada da: Farfesa Wale Oladipo (Osun) wanda ya nuna sha’awarsa ga mukamin Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Uche Secondus garzaya kotu don hana gangamin taron PDP na ƙasa

Hakazalika da Okey Muo-Aroh (Anambra) wanda ya nuna sha’awar matsayin Sakataren Kasa Dakta Olafeso Eddy (Ondo) Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel