‘Yan Igbo za su bar Najeriya ne a duk lokacin da suka ga dama – Ohanaeze ta caccaki kungiyar arewa

‘Yan Igbo za su bar Najeriya ne a duk lokacin da suka ga dama – Ohanaeze ta caccaki kungiyar arewa

  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta mayar da zazzafan martani ga hadakar kungiyoyin arewa da suka nemi kotu ta kore su daga Najeriya
  • A cewar kungiyar, yan kabilar Igbo za su bar kasar ne a lokacin da suka ga dama
  • Ohanaeze ta ce yan kabilar sun sadaukar da abubuwa fiye da kowace kabila a kasar don haka babu mai iya korarta daga cikinta

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cewa ‘yan kabilar Igbo za su bar Najeriya ne a duk lokacin da suka ga damar yin hakan.

Ta bayyana hakan ne yayin da take martani ga karar da wasu kungiyoyin arewa suka shigar gaban babbar kotun tarayya ta Abuja inda suka nemi a kori yan kudu maso gabas daga Najeriya.

‘Yan Igbo za su bar Najeriya ne a duk lokacin da suka ga dama – Ohanaeze ta caccaki kungiyar arewa
‘Yan Igbo za su bar Najeriya ne a duk lokacin da suka ga dama – Ohanaeze ta caccaki kungiyar arewa Hoto: Igbo voice
Asali: Facebook

Dattawan arewa sun nemi a kori yan yankin ne saboda barna da rikicin da ake zargin yan awaren IPOB da aikatawa.

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

Kakakin kungiyar Ohanaeze wanda ya zanta da jaridar Punch ta wayar tarho, ya bayyana kungiyar a matsayin makirai, inda ya kara da cewa yan Igbo na da asali da salsala fiye da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ogbonnia ya kuma bayyana cewa babu wanda ya fi wani karfi ko wanda ke gaba da wani a Najeriya, saboda haka ya ce babu wata kungiya da za ta dunga nuna fifiko ko ganin tana gaba da wani a Najeriya, Sahara Reporters ta kuma rahoto.

“Kuma saboda babu kungiyar da ke da yancin korar wata daga Najeriya, yan kabilar Igbo na da ‘yanci kamar kowacce kabila a Najeriya. Kuma saboda haka, yan Igbo za su bar Najeriya ne kawai a lokacin da suka ga damar yin haka ba wai bisa umurnin wata kungiya ba.
“A daya bangaren, yan Igbo sun sadaukar da abubuwa da dama fiye da kowace kungiya don wanzuwar Najeriya. Na maimaita, Igbo sun sadaukar da abubuwa da dama fiye da kowace kungiya don wanzuwar Najeriya kuma bata shakku.

Kara karanta wannan

Shugaban 'yan bindiga, Shehu Rekeb, ya sanar da dalilinsu na kai farmakin Goronyo

"Don haka, idan akwai kungiyar da ya kamata ta yi magana game da mallakar kasar nan toh wadanda suka sadaukar sosai ne."

Kan fafutukar da masu neman ballewa a kudu maso gabas ke yi, kakakin na Ohanaeze ya ce tushen dukka matsalolin shine cewa yan Igbo na neman ayi masu adalci da daidaito.

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

A baya mun kawo cewa wata tawagar dattawa daga Arewacin Najeriya ta nemi babban kotun tarayya reshen Abuja da a roki 'yan majalisu a Najeriya su cire yankin kudu maso gabas daga Najeriya kafin aiwatar da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin Najeriya.

Nastura Ashir Shariff, Balarabe Rufa’I, Abdul-Aziz Sulaiman da Aminu Adam sun shigar da batun kotu tare da bayyana cewa, hakan zai taimaka wajen rage faruwar rikice-rikice da zubar da jinane a daga 'yan awaren yankin.

Kara karanta wannan

Shugaban Turkiyya ya gargadi Buhari, ya ce ya kula da masu shirin juyin mulki

Sun yi ikirarin cewa ba sa son a maimaita yakin basasar da aka yi a Najeriya tsakanin 1967 zuwa 1970 wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar da yawansu ya kai biliyoyin Naira, Daily Sun ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel