Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

sokacin Edita: Abu ne sananne duk wanda a kammala karatuj jami'a a Najeriya ya kokarta wajen shiga shirin NYSC, amma shin wadanne irin batutuwa ne ke tattare da shirin na NYSC? Rahoton da muka tattar a bayyana bayanai kan lamarin tsaro da halin da ake ciki.

Al-Jazeera ta rahoto cewa, wata rana, da misalin Karfe 3 na yamma ranar Lahadi a tsakiyar watan Mayu lokacin da Kelechi, wani dan shekara 27 ya leka ta tagar motar fasinja mai fasinja 18 da yake tafiya aciki.

Kelechi mai digiri da ya kammala karatu a jami’ar Calabar da ke jihar Cross River, yana kan hanyarsa ta zuwa Benue, wacce ta zama cibiyar hare-hare daga kungiyoyi 'tan ta'adda da ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Bincike: Yadda Ministan Buhari yake amfani da kujerarsa yana yin abin da ya ga dama a mulki

Gwamnatin jihar Benue ta haramta hawa babura a yankin tare da kafa shingayen bincike akan tituna. Amma yayin da karamar motarsu ta shiga jerin gwanon ababen hawa a wurin binciken ababen hawa, Kelechi ya ga babur yana zuwa.

Rashin tsaro da dardar: Sansanin NYSC ya zama abin tsaro ga matasan bautar kasa
Sansanin NYSC | Hoto: ajzaeera.com
Asali: UGC

Mutanen da ke kan babura na dauke da bindigogi. Nan da nan suka bude wuta, inda suka kashe mutane biyu.

Kelechi da ya tuno lamarin, yana mai bayanin yadda mutanen suka hau babur dinsu suka gudu.

Lokacin da Kelechi ya isa gidansa, ya tuna abin da ya gani kuma ya fahimci "watakila da ni ne [wanda aka kashe]".

A wannan daren da daren da ya biyo baya, ya yi fama da rashin bacci kamar yadda abin da ya gani a wannan ranar ya dinga zuwa a zuciyarsa.

Kara karanta wannan

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

A yadda aka saba, Kelechi zai iya kasancewa a gida a Calabar, inda ya girma cikin danginsa masu hannu da shuni.

Amma lokacin da ya kammala karatu daga jami'a, an shigar da shi cikin masu hidimar bautar kasa ta kasa (NYSC), inda aka turashi jihar Benue.

Dokar Najeriya ta ba da izinin kammala shirin shekara guda tare da NYSC, tare da kakaba tara ko daurin kurkuku a matsayin hukunci ga wadanda suka ki yin hakan, ko da yake masana sun ce ba a taba aiwatar da wannan hukunci ba.

A wani bangare na shirin, wanda ke zama dole ga wadanda ke son yin aiki da gwamnati da wasu kamfanoni masu zaman kansu, ana tura membobin bautar kasa nesa da garinsu.

Manufar ita ce samar da hadin kai da zaman lafiya tsakanin al'ummomi. A musayar hakan, membobin bautar suna samun alawus na wata-wata daga gwamnati.

Ko da yake wasu masu digiri sukan nemi hanyoyin tsallake shirin, yawancin 'yan Najeriya masu aiki-wadanda daman aikin su ya riga ya takaita-ba za su iya sadaukar da damar da ke tattare da takardar shaidar NYSC ba.

Kara karanta wannan

Kallo ya koma sama: Bidiyon ango ɗan Nigeria sanye da siket yana tiƙa rawa a ranar aurensa ya ɗauki hankula

Wannan shine dalilin da ya sa Kelechi ya shiga shirin NYSC a 2019. Amma damar kwarewar ba ta kasance abin da ya zata ba.

Lokacin da ya fara nema, an tura shi jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya, kusa da yankin Arewa ta tsakiya, tsakanin arewa da kudu - yankin da ke fama da rikice-rikicen kabilanci da na 'yan bindiga.

Amma, bayan watanni uku kacal yana koyarwa a makarantar sakandare a can, ya tafi. Rikici tsakanin kabilu daba -daban a yankin ya sa ya ji tsoron abin da zai faru da rayuwarsa, in ji shi.

A cewarsa:

"Na yi kokarin canza wuri zuwa wata jiha, amma hakan bai yi tasiri ba kuma iyayena sun ce ba a shirye suke su rasa dansu ba."

A cikin 2020, ya sake nema, amma sai cutar Korona ta bulla inda aka dakatar da wasu bangarorin shirin na dan lokaci. Ya sake gwadawa a 2021, wanda shine lokacin da aka tura shi Benue.

Kara karanta wannan

Rahoto: Sojoji 10 da wasu mutum 21 sun mutu a harin yan bindiga cikin mako ɗaya a Najeriya

Lokacin da ya tuntubi wani jami'in NYSC game da harbin da ya gani, ya ce sun gaya masa cewa babu abin da za su iya yi game da haka, kuma ya kamata ya yi taka-tsantsan ya kuma kula.

Ko da yake membobin bautar suna samun ta cewa kan cikin irin wuraren da aka tura su, ba za su iya yin watsi da tura su da aka yi ba.

Lokacin da aka tambaye shi yayi sharhi kan dalilin da ya sa ake tura masu yi wa kasa hidima zuwa yankunan da ba su da tsaro, kakakin NYSC ya amsa ta sakon tes cewa:

“NYSC ba ta tura 'yan bautar kasa zuwa jihohin da ba su da tsaro; akwai hadin kai tsakanin shirin da hukumomin tsaro kuma ana sanya membobin kungiyar bisa matakan tsaro daga hukumomin tsaro da suka dace."

Gyara raunukan yaki a Najeriya

Lokacin da aka kirkiro NYSC a 1973, shekaru uku bayan kawo karshen yakin basasar Najeriya, manufarsa ita ce ta gyara raunukan yakin da ya faru da cusa ruhin gina kasa a zukatan 'yan Najeriya, musamman matasa.

Kara karanta wannan

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

A cewar wani tsohon babban darakta na shirin, wadanda suka kammala karatun digiri 300,000 (daga jami’o’in gwamnati da masu zaman kansu da kwalejojin kimiyya) ana tara su duk shekara don shiga shirin na NYSC inda ake tura su wasu sassan kasar.

Rashin tsaro da dardar: Sansanin NYSC ya zama abin tsaro ga matasan bautar kasa
Sansanin NYSC | Hoto: ajzaeera.com
Asali: UGC

Duk membobin bautar kasa da farko suna fara yin aikin tilas na sati uku na horon irin na soja da sana'a a karkashin Sashin Samun Kwarewa da Kasuwanci (SAED), a sansanin NYSC a duk fadin kasar.

Manufar shirin SAED shine ba membobi karin kwarewa wadanda zasu iya sa su sami aiki ko inganta makomar tattalin arzikin su na gaba. Da wannan a zuciyarsu, ana koya musu abubuwa kamar girki, hada takalmi, jaka, zane, da dinki da dai sauransu.

Bayan zaman sansanin, ana tura su zuwa wurin aiki (PPA) na shekara guda, akan alawus na kowane wata na naira 33,000. Ya danganta da wurin da suke, membobin na iya samun karin kuki kai tsaye daga PPA din su.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi kuka kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya roki Allah da Ya hukunta maharan

A shekarar 2020, an ware kimanin naira biliyan 161 na kudin gwamnati saboda shirin. Sai dai, yayin da tattalin arzikin Najeriya ke tabarbarewa kuma damar masu karatun digiri ta ragu, wasu masana da membobin bautar kasa sun yi shakku kan ingancin shirin.

A bangare guda, wasu mambobin NYSC kan koka kan yadda ake rike su a wuraren da suke aiki, inda wasu ke cewa ba a basu ainihin abin da suka karanta a jami'ia.

Bayan kammala wannan dogon zama na shekara guda a jihar da ba ta mambobinba, daga nan akan ba da takardar shaidar kammala shirin ga wadanda suka kammala.

A wani sabon batu, an samu wani mamban majalisa da ya nemi gwamnati ta gaggauta soke shirin NYSC din gaba daya.

Hakazalika, wasu mambobin sukan bayyana bukatar gwamma su zauna gida sabanin ci gaba da shirin, wanda a cewarsu, bata lokaci ne kawai.

Duba da wasu abubuwa da suke faruwa, musamman ta fuskar tsaro, shirin NYSC na iya zama abin tsoro ga da yawa daga cikin 'yan Najeriya a sassa daban-daban na kasar.

Kara karanta wannan

Ku ba 'yan bindiga hadin kai don tsira da rayukanku, shawarin 'yan sanda ga 'yan Najeriya

Ga dai matsaloli da ke tattare da shirin NYSC, a hakan ya dace a ci gaba da shirin? kuma shirin shin yana tasiri?

Masari ya janye ra'ayinsa kan bindiganci, ya nemi a ayyana dokar ta-baci kan rashin tsaro

A bangare guda, Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya roki gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta-baci a kan rashin tsaro.

Bukatar tasa na zuwa ne watanni bayan da ya yi watsi da kiran da majalisar wakilai ta yi a watan Afrilu, inda suka nemi gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-baci kan rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel