Shugaban 'yan bindiga, Shehu Rekeb, ya sanar da dalilinsu na kai farmakin Goronyo

Shugaban 'yan bindiga, Shehu Rekeb, ya sanar da dalilinsu na kai farmakin Goronyo

  • 'Yan bindigan Sokoto da na Zamfara sun hada kai tare da kai farmaki kasuwar Goronyo inda suka halaka rayuka 49
  • Shehu Rekeb, gagararren shugaban 'yan bindiga ya ce sun yi hakan ne domin fansar rayukan Fulani da ake kashewa a Goronyo
  • Kamar yadda ya ce, sun ji shugaban kasa ya kira su da dabbobi, toh su kuwa ba dabbobi bane kuma fansa suka dauka

Sokoto - 'Yan bindiga da ke karakaina tsakanin jihohin Sokoto zuwa Zamfara sun dauka alhakin kai farmakin kasuwar Goronyo a jihar Sokoto inda suka halaka rayuka 49 a ranar Lahadin da ta gabata.

Daya daga cikin gagararrun 'yan bindigan da ke da kusanci da Kachallah Turji da Halilu Sububu, manyan miyagun yankin, mai suna Shehu Rekeb, ya ce sun kai wannan farmakin ne domin daukar fansa kan kisan Fulani da ake yi a yankin.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Yadda 'yan bindiga suka yi wa jama'a kisan kiyashi a kasuwar Sokoto

Shugaban 'yan bindiga, Shehu Rekeb, ya sanar da dalilinsu na kai farmakin Goronyo
Shugaban 'yan bindiga, Shehu Rekeb, ya sanar da dalilinsu na kai farmakin Goronyo. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A ranar Talatar da ta gabata Daily Trust ta ruwaito cewa, farmakin na hadin guiwa ne saboda yadda sama da babura dari suka tsinkayi kasuwar kuma suka bude wa jama'ar wuta.

Sun zagaye dukkan kasuwar tare da budewa masu siye da siyarwa wuta, lamarin da ya kawo mutuwar rayuka arba'in da tara.

"Mun ji an kwatanta wadanda suka kai farmakin Goronyo da dabbobi, Mu ba dabbobi ba ne.
"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fito ya ce hakan. Jama'ar Goronyo sun kashe mutane da yawa, saboda haka ne muka kai musu farmaki tare da kashe su," yace.

Ya bada misali da yadda aka kashe Fulani Musulmai yayin da suke bauta a Unguwar lalle.

Rekeb ya ce, "A lokacin da aka kashe wadannan Fulanin, shugaban kasa bai ce komai ba amma yanzu ya fito ya na martani kan wannan."

Kara karanta wannan

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

Wani mazaunin yankin a ranar Litinin ya sanar da Daily Trust cewa, "wannan farmakin Goronyo ba zai rasa alaka da harin daukar fansa ba kan 'Yan Sa Kai' saboda kashe makiyaya 11 da suka yi a kasuwar Mamande da ke karamar hukumar Gwadabawa ta jihar.
“Wadannan mutanen na kamawa tare da kashe Fulani babu dalili," yace.

Dalla-dalla: Yadda 'yan bindiga suka yi wa jama'a kisan kiyashi a kasuwar Sokoto

A wani labari na daban, kisan kiyashin da 'yan bindiga suka yi wa jama'a a kasuwar Goronyo da ke gabashin jihar Sokoto a daren Lahadi ya tada hankula.

Ganau sun sanar da Daily Trust a ranar Litinin cewa, mummunan farmakin da aka kai ya kunshi 'yan ta'adda daga mabanbantan kungiyoyi.

Sun ce miyagun sun ajiye banbancinsu tare da hada kai inda suka tsinkayi kasuwar mako-mako ta Goronyo suka dinga harbe-harbe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel