Shugaban Turkiyya ya gargadi Buhari, ya ce ya kula da masu shirin juyin mulki

Shugaban Turkiyya ya gargadi Buhari, ya ce ya kula da masu shirin juyin mulki

  • Shugaban kasar Turkiyya ya gana da shugaba Buhari, ya bayyana wasu abubuwa game da kifar da gwamnatinsa
  • Ya ce, wadanda suka kitsa kifar da gwamnatinsa a Turkiyya suna nan a Najeriya suna ci gaba da rayuwa
  • Ya kuma nemi gwamnatin Buhari ta hada kai da tasa wajen yaka da fatattakar 'yan ta'adda a kasashen biyu

Abuja - Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya ya nuna damuwa cewa har yanzu kungiyar 'yan ta'adda ta Fetullah (FETO), wanda ya zarga da yunkurin masa mulkin ba a ranar 15 ga watan Yulin 2016, ya ce su ne a Najeriya.

Da dumi-dumi: Shugaban Turkey ya gana da Buhari, ya bayyana masa masu son rusa Najeriya
Shugaba Buhari da shugaban Turkey | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Erdo spokean ya yi magana ne ranar Laraba a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Shugaba Muhammadu Buhari a yayin ziyarar aiki a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin muhimman abubuwa 7 daga ganawar Buhari da shugaban kasar Turkiyya

Shugaban ya gabatar da jawabinsa ne cikin yarensa na Turkiya wanda daya daga cikin jami'ai da ke tawagarsa ya fassara.

Erdogan ya nemi Najeriya da ta hada kai da kasarsa don samar da hadin kai a yaki da ta'addanci a kasashen biyu kasancewar Najeriya tsohuwar kawa gaTurkiyya a Afirka na tsawon shekaru 60 na dangantakar diflomasiyya.

Ya ce:

“Ya ku 'yan jarida, a matsayinmu na Turkiyya, muna sanya ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya, ‘yan uwanmu kuma abokanmu.

Da yake magana kan yawaitar ta'addanci da kuma yiyuwar daukar mataki, ya buga misali da kasarsa, inda yace:

"Kamar yadda watakila muna sane da cewa Turkiyya tana yaki da kungiyoyin ta'addanci shekaru da yawa, kamar PKK, PYD, FETO, DASH da sauran kungiyoyin ta'addanci.

Kara karanta wannan

APC da PDP ba za su taba sauyawa ba: Jega ya bayyana matsalolin APC da PDP

“Wadanda ya kitsa mummunan juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 15 ga Yuli, FETO, har yanzu suna aiki ba bisa ka’ida ba a Najeriya, kuma muna ci gaba da raba bayananmu ga masu tattaunawa da hukumomi na Najeriya.
"Ina fata kuma ina addu'a cewa 'yan uwanmu na Najeriya za su kulla hadin kai a wannan fanni tare da mu, Jamhuriyar Turkiyya.
"Ina fata da addu’a cewa ziyarar mu za ta haifar da sakamako mai kyau kuma ina son in gode wa fitaccen dan uwana, Shugaba Buhari, saboda kasancewarsa mai masaukin baki mai kyau a gare ni da wakilai na."

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan bindiga cewa su kasance a shirye don murkushe su ya zo kusa.

Shugaban ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin 18 ga watan Oktoba yayin da yake mayar da martani kan kisan sama da mutane 30 a Goronyo, Jihar Sakkwato ranar Lahadi.

Buhari, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, ya ce kwanakin 'yan bindiga a kirge suke saboda karfin da sojojin Najeriya ke samu ta hanyar samun kayan aiki da sauran bukatu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel