Ma'aikatar Lafiya na shirin karban bashin N82bn don sayen ragar kariya daga cizon sauro

Ma'aikatar Lafiya na shirin karban bashin N82bn don sayen ragar kariya daga cizon sauro

  • Gwamnatin Buhari zata ciyo bashin bilyan 82 don sayen ragar kariya da cizon sauro a shekarar 2022
  • Wannan na kunshe cikin kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya
  • Yan majalisar kuwa sun ce gaskiya ba zasu yarda da wannan abu ba, dole sai an sake dubawa

Abuja - Majalisar dattawar Najeriya ta yi Alla-wadai da shirin da ma'aikatar kiwon lafiyan Najeriya ke yi na karban bashin $200 million (N82,070,388,916.76) a kasafin kudin shekarar 2022.

Ma'aikatar za ta amfani da wannan bashi ne wajen sayawa yan Najeriya ragar kariya daga cizon sauro, rahoton SR.

Sakaraten din-din-din na ma'aikatar ya bayyanawa kwamitin a taron bayani kan kudin da ma'aikatar ta bukata cikin kasafin kudin 2022.

Daya daga cikin mambobin kwamitin kiwon lafiya na majalisar dattawa, Gershom Bassey, ranar Talata ya ce sam ba dashi za'a yi wannan ba.

Kara karanta wannan

Jerin tafiye-tafiye 9 da shugaba Buhari ya yi zuwa kasashen waje a shekarar 2021

Bassey ya laburtawa Sakaraten din-din-din na ma'aikatar cewa wannan kudi na bilyan 82 da ake shirin karba bashi don sayan ragar Malariya yayi yawa.

Kwamitin ta bukaci Sakataren ya tattaro mata dukkan bukatan ma'aikatar domin tabbatar da cewa lallai suna bukatan wannan bashi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ma'aikatar Lafiya na shirin karban bashin N82bn don sayen ragar kariya da cizon sauro
Ma'aikatar Lafiya na shirin karban bashin N82bn don sayen ragar kariya da cizon sauro

Jagoran sayo rigakafin Korona ya yi tsokaci

Diraktan hukumar cigaban kiwon lafiya na kananan asibitoci, Faisal Shuaib, a jawabinda yace wannan kudi da za'a karba bashi na shigo da ragar ne daga kasar waje da kuma hada wasu a nan Najeriya.

Amma shugaban kwamitin kiwon lafiya, Sanata Ibrahim oloriegbe a martaninsa yace wannan fa kawai so ake a rabon kudi tsakanin juna.

Bayan shekaru 30 ana bincike, an samu rigakafin ciwon zazzabin cizon sauro, Malariya

Kungiyar Lafiyar Duniya (WHO) ta amince da rigakafin RTS,S/AS01 (RTS,S) na ciwon zazzabin sauro watau Malariya don yiwa kananan yara a nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya hannun yan daba a majalisar dokokin jihar Zamfara

Tedros Ghebreyesus, shugaban WHO, ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Laraba, 6 ga Oktoba, 2021.

Wannan ya biyo bayan gwajin da aka kwashe shekaru biyu ana yi kan kananan yara a kasashen Ghana, Kenya da Malawi.

Tedros Ghebreyesus ya bayyana cewa wannan sabon rigakafin zai taimaka wajen rage zazzabin cizon sauro a nahiyar Afrika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel