Bayan shekaru 30 ana bincike, an samu rigakafin ciwon zazzabin cizon sauro, Malariya
- Bayan shekara da shekaru, an samu rigakafin zazzabin cizon sauro a duniya
- An yi gwajin wannan rigakafi kan yara a kasashe 3 dake nahiyar Afrika
- An kwashe shekaru 30 ana bincike kuma an yi shekaru biyu ana gwaji
Kungiyar Lafiyar Duniya (WHO) ta amince da rigakafin RTS,S/AS01 (RTS,S) na ciwon zazzabin sauro watau Malariya don yiwa kananan yara a nahiyar Afrika.
Tedros Ghebreyesus, shugaban WHO, ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Laraba, 6 ga Oktoba, 2021.
Wannan ya biyo bayan gwajin da aka kwashe shekaru biyu ana yi kan kananan yara a kasashen Ghana, Kenya da Malawi.
Tedros Ghebreyesus ya bayyana cewa wannan sabon rigakafin zai taimaka wajen rage zazzabin cizon sauro a nahiyar Afrika.
Yace:
"Wannan lokacin tarihi ne. Rigakafin Malariya na yara da aka dade ana sauraro tarihi ne ga ilimin Kimiya, kiwon lafiyan yara da kuma kawar da Malariya."
"Amfani da wannan rigakafin da magungunan da ake da su zasu taimaka wajen ceton rayukan dubban yara."
Bill Gates ya bada gudunmuwa matuka
A cewar WHO, an kwashe shekaru 30 ana bincike kan rigalafin kuma an samu gudunmuwa daga kungiyoyi irinsu PATH, UNICEF, da GlaxoSmithKline (GSK), da zasu bada kyautan allurai milyan 10 a fari.
WHO ya ce ta samu kudin bincike daga wajen gidauniyar Bill Gates tsakanin 2001 da 2015.
Zamu fara tilastawa ma'aikatan gwamnati yin allurar rigakafin Korona, SGF Boss Mustapha
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata tilastawa ma'aikatan gwamnatin yin rigakafin Korona.
Yace amma ba za'a wajabtawa gama-garin yan Najeriya yin allurar rigakafin har si an samar da isasshen rigakafi da kowa zai samu.
Yace:
"Ko shakka babu za'a tilastawa mutane yin allurar rigakafin Korona. Muddin kasashen Turai suka gama yiwa al'ummarsu rigakafin Korona, ba za ka iya zuwa ba sai ka yi.
Wannan tuni ya fara faruwa." "Dalilin da yasa zamu wajabtawa ma'aikatan gwamnati yin rigakafin shine zasu rika tafiye-tafiye a madadin gwamnatin tarayya."
Asali: Legit.ng