Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya hannun yan daba a majalisar dokokin jihar Zamfara

Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya hannun yan daba a majalisar dokokin jihar Zamfara

Mamban majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltan Arewacin Talata-Mafara, Hanarabul Shamsudden Hassan, ya tsallake rijiya da baya ranar Alhamis a zauren majalisar.

Wannan abu ya auku ne yayin taron tantance mutum biyu da gwamnan jihar ya gabatar da sunayensu don tabbatar da su matsayin kwamishanoni a gwamnatinsa, rahoton Punch.

Dan majalisan ya nuna rashin goyon bayansa kan daya daga cikin wadanda gwamnan ya turo sunayensu, Hajiya Rabi Ibrahim Shinkafi, wacce ta rike mukamin mai baiwa gwamna Matawalle shawara.

Hanarabul Shamsudden ya bayyana cewa shi dai bai goyon bayan nadinta matsayin kwamishanan a gwamnatin Matawalle saboda gajiyayya ce.

A cewarsa:

"Idan wannan gidan za ta tantanceta ne bisa ayyukan da tayi a baya, toh lallai ba zata ketare ba saboda ko maki daya ba ta samu."

Kara karanta wannan

Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa

Amma kafin ya kammala jawabinsa, wasu matasa sun dira kansa suka dura masa ashar kuma suna jifansa inda suka ce yayi shiru ko kuma ya sha dukan tsiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bai cin jami'an tsaron da suka kareshi, da matasan sun koyawa dan majalisar darasi, cewarsu.

Dan majalisa ya tsallake rijiya da bayan hannun yan daba a majalisar dokokin jihar Zamfara
Dan majalisa ya tsallake rijiya da bayan hannun yan daba a majalisar dokokin jihar Zamfara
Asali: UGC

Sakamakon haka, majalisar daga yanzu ta haramtawa mabiyan yan siyasa shiga cikin majalisa.

Diraktan yada labaran majalisar, Mustafa Jafaru Kaura yace:

"Bamu ji dadin abinda mabiya yan siyasan da gwamnati ta kaddamar suke yi ba lokacin tantancesu, daga yau majalisa ta yanke shawara haramta musu halartan zaman majalisa."
"Mun yanke wannan shawara ne a anan majalisar yau yayinda wasu yan majalisa suka bayyana ra'ayoyinsu kan abinda wasu kwamishanoni da gwamnan Bello Mohammed yayi."

Tsokaci kan lamarin, shugaban masu rinjaye a majalisa, Faruk Musa Dosara, sun yi Alla-wadai da abinda ya faru.

Kara karanta wannan

Muna farin cikin soke dokokin COVID-19 a Masallacin Makkah da Madina: Hukumar jin dadin Alhazai

Asali: Legit.ng

Online view pixel