Gwamnatin Buhari ta lashi takobin tsamo 'yan Najeriya Miliyan 2 daga jahilci duk shekara

Gwamnatin Buhari ta lashi takobin tsamo 'yan Najeriya Miliyan 2 daga jahilci duk shekara

  • Gwamnatin tarayya ta sha alwashin tsamar da ‘yan Najeriya miliyan 2 daga jahilci don su daukaka
  • Sakataren hukumar yaki da jahilci ta NMEC, Farfesa Simon Ibor Akpama ya bayyana hakan
  • A cewarsa, sakamakon rashin kayan aiki, yanzu ana kokarin koya da mutane 11,000 cikin watanni 7

Jihar Imo - Gwamnatin tarayya ta shirya kaddamar da shirin ta na ilimantar da ‘yan Najeriya miliyan 2 duk shekara don daga mu su darajar su wurin samar da ci gaban kasa a ruwayar Vanguard.

Sakataren hukumar yaki da jahilci ta NMEC, Farfesa Simon Ibor Akpama ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin tallafa wa kauyaku ta RFS a Owerri, jihar Imo.

Gwamnatin Buhari ta lashi takobin tsamo 'yan Najeriya Miliyan 2 daga jahilci duk shekara
Gwamnatin Buhari ta lashi takobin tsamo 'yan Najeriya Miliyan 2 daga jahilci duk shekara. Hoto: Vanguard NGR
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

Vanguard ta ruwaito yadda Farfesa Akpama ya bayyana cewa sakamakon halin da kasa ta ke ciki na rashin kayan aiki da kudi ake shirin ilimantar da mutane 11,000 cikin watanni 7.

A cewar sa gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin ne musamman don nuna muhimmancin ilimi.

A cewar sa, za a fi mayar da hankali akan Owerri babban birnin jihar Imo, Ibadan dake jihar Oyo da Kano. An shirya shirin ne don daga tutar bangarorin ilimin a makarantu da gidaje.

Ya lissafo matsalolin da su ke fuskanta ciki har da rashin samar da kudaden da za ayi amfani da su daga jihohi da kuma rashin yawan masu koyarwar da za su iya dacewa da yawan matasa da manyan da ba su iya karatu ba.

Farfesa Akama ya kara da cewa wannan babbar damuwa ce kuma shi ya ke hana cikar burin majalisar dinkin duniya na 4 na samar da ilimi ga kowa.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: ‘Yan bindiga sun cinna wuta a fadar sarkin Imo

Ya ce hukumar ta na kokarin nuna darajar ilimi

A cewar sa hukumar tana iyakar kokarin ta a kauyaku wurin kwatanta muhimmancin ilimi don kawar da jahilci ga matasa da manya.

Kamar yadda ya shaida:

“Gabadaya makasudin shirin shi ne tallafa wa rayuwar matasa da manya wadanda ba su taba zuwa makaranta ba don su iya rubutu da karatu.
“Akwai wadanda yanayin rayuwa, ciki ga mata, rashin lafiya, mutuwar iyaye ko kuma barin makaranta da wuri ya hana su damar tara ilimi.
“Don haka za a gabatar mu su da dama wacce za su gusar da rashin iya karatu, rubutu, kirga da sauran su don su yi ingantacciyar rayuwa.”

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Kara karanta wannan

Muna farin cikin soke dokokin COVID-19 a Masallacin Makkah da Madina: Hukumar jin dadin Alhazai

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel