Muna farin cikin soke dokokin COVID-19 a Masallacin Makkah da Madina: Hukumar jin dadin Alhazai

Muna farin cikin soke dokokin COVID-19 a Masallacin Makkah da Madina: Hukumar jin dadin Alhazai

  • Gwamnatin kasar Saudiyya ta sassauta dokokin kariya daga COVID-19 a Makkah da Madina
  • Daga farkon makon nan, an cigaba da hada sahu a Masallatan biyu
  • Hukumar NAHCON a Najeriya tayi tsokaci kan wannan lamari

Hukumar jin dadin alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana farin cikinta bisa soke dokokin kariya daga cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Saudiyya take a farkon makon nan.

Kwamishanan hukumar mai wakiltar al'ummar yankin kudu maso kudu, Musa Sadiq Oniyesaneyene, ya bayyana hakan a hirarsa da Legit Hausa.

A cewarsa, ba hukumar kadai ba, dukkan Musulman Najeriya ma sun yi farin ciki da wannan sanarwa.

Dokokin da gwamnatin kasar ta sanya na tsawon shekara daya da rabi sun hada da takaita adadin Masallata da Mahajjata, da wajabta bayar da tazara tsakanin jama'a.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin Buhari: Za a sayi janareta na N104bn, aikin wutar Mambila kuma N650m

Ya kara da cewa wannan alama ce dake nuna Allah (SWT) ya karbi addu'o'in da suke yi don kawar da annobar Korona daga cikin al'umma.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yayinda muka samu labarin soke dokokin, wallahi mun yi farin ciki, amma na san yawancin Musulman Najeriya ma sun ji dadi saboda tsawon shekaru biyu yanzu an take musu hakkinsu na zuwa aikin Hajji sakamakon annobar COVID-19 da ta mamaye duniya."
"Wallahi kowa yaji dadi, abin alkhari ne. Ya kamata muce 'Alhamdulillah' saboda Allah ya karbi addu'o'in da muka dade munayi, azumin da mukeyi don komai ya dawo daidai."

Muna farin cikin soke dokokin COVID-19 a Masallacin Makkah da Madina: Hukumar jin dadin Alhazai
Muna farin cikin soke dokokin COVID-19 a Masallacin Makkah da Madina: Hukumar jin dadin Alhazai Sadiq/Haramain
Asali: Facebook

An daina bada tazara a sahun Sallah daga Lahadi a Makkah da Madina

Hukumomi a Masallatai biyu mafi daraja a duniya sun yi watsi da dokar wajabta baiwa juna tazara yayin Sallah a Masallacin Haram dake Makkah da Masjid Al Nabawi dake Madina.

Kara karanta wannan

Bidiyon limamin Makkah na kira a daidaita sahu, karon farko sama da shekara guda

An yi watsi da wannan doka ne fari daga ranar Lahadi, 17 ga watan Oktoba, 2021.

Sheikh AbdulRahman Sudais ne shugaban Masallatan Biyu.

Wata majiya a fadar Sudais ta bayyana cewa za'a cire dokar bada tazaran ne daga ranar Asabar bayan Sallar Isha, rahoton Haramain Sharifain.

Bidiyon limamin Makkah na kira a daidaita sahu, karon farko sama da shekara guda

A cikin wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta samo a shafin Haramain Sharifain na Facebook, an limamin masallacin Harami yana kira da a daidaita sahu, a hada kafadu da kuma cike gibi.

"Bayan shekara daya da rabi… Sheikh Baleelah yayi kira da a daidaita sahu, a cike gibi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel