A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

  • Wata Firdausi Sulaiman ta maka mijinta Haruna Haruna a kotu tana bukatar a raba auren su
  • Kamar yadda ta bayyana wa kotu, har bugun ta yake yi saboda tana da mugun cin abinci
  • A cewar Firdausi, har rufe kicin yake yi da dare sannan mahaifiyarsa ta ce yana fama da bakaken aljanu

Jihar Kaduna - A ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin ya ke yi da dare, Matar aure ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta
Mata da Miji. Hoto: NewsWireNGR
Asali: Facebook

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi na karfafa fashi da makami a arewa, Kungiyar CAN ta yi zargi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Firdausi ta ce bai taba yin shekara 1 bai fatattake ta gidan iyayen ta ba

Firdausi ta shaida wa kotu cewa:

“A shekaru 7 da muka yi da aure, ban taba yin shekara daya cur ba, ba tare da ya fatattake ni gidan iyaye na ba.
“Dama auren dole mahaifi na ya yi min da Haruna lokacin ina da shekaru 16.
“Ya hana ni amsar baki a gidan auren mu sannan yana lakada min dukan tsiya.
“Bayan na gaji da azabar na sanar da iyaye na abinda yake faruwa sai suka shawarce ni da in sanar da iyayen sa. Mahaifiyar sa ta ce bakaken aljanu ne suke damun sa."

Ta bukaci kotu ta raba auren su kuma ta bata damar rike diyar su daya.

Lauyan Haruna ya ce lafiyar sa kalau

A bangaren Haruna, wanda injiniya ne, ta bakin lauyan sa, M. K Mustapha ya ce lafiyar wanda yake karewa kalau kuma babu wani aljanun da suke damun sa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda za su gurfanar da wata matashiya ‘yar shekara 25 da ke yi wa ‘yan bindiga leken asiri a Katsina

A cewar lauyan:

“Wanda nake karewa ba ya kama da mai aljanu ko kuma mai tabin hankali. Yanzu haka yana jihar Katsina yana ayyukan sa na kwangila.”

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Ya umarci Lauyan Haruna ya gayyaci iyayen wadanda ake shari’ar akan su ko kuma magabatan su don ganin yadda za a bullo wa lamarin.

Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa

A wani labarin daban, wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.

Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.

Kara karanta wannan

Daga bisani, NAF ta dauka alhakin yi wa farar hula ruwan wuta a Yobe

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel