Wurin neman aiki, budurwa taci karo da wanda ta damfara N500,000 shekaru 5 da suka wuce, ya koya mata darasi

Wurin neman aiki, budurwa taci karo da wanda ta damfara N500,000 shekaru 5 da suka wuce, ya koya mata darasi

  • Wani Ikechukwu Diamond ya samu damar kara haduwa da wacce ta damfare shi N500,000 shekaru 5 da su ka wuce
  • Saidai, maimakon ya fatattake ta ko ya ci zarafin ta a wurin ya dakatar da kowa daga fita sannan ya ba ta dama
  • Ta durkusa gwiwoyin ta 2 a kasa ta na zubar da hawaye wanda hakan ya janyo ya yafe mata har da rungume ta

Wani mutum dan Najeriya ya nuna karamci ga wata budurwa wacce ta damfare shi N500,000 tun shekaru 5 da su ka shude.

Ikechukwu Diamond, a cikin wata wallafa mai tsawo da ya yi a LinkedIn, ya bayyana matar ta zo neman aiki a wani kamfani da ya ke cikin masu daukar aikin.

Read also

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

Wurin neman aiki, budurwa taci karo da wanda ta damfara N500,000 shekaru 5 da suka wuce, ya koya mata darasi
Na yafe mata, mutumin da ya hadu da wadda ta damfare shi N500,000 shekaru biyar da suka wuce. Hoto: Ikechukwu Diamond
Source: UGC

Tana shigowa harabar wurin ya gane ta daga nan ya umarci jami’an tsaron kamfanin da kada su bar kowa ya fita daga wurin.

Ta yi matukar mamakin yadda ya yi bayan lokacin da za su tattauna ya bata dama duk da ta tabbatar ya gane ita ce ta damfare shi a baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta na ganin haka ta durkusa gwiwoyi bibbiyu tana hawaye. Ba tare da ta yi zato ba, mutumin ya rungume ta ya kwantar ma ta da hankali.

Ya ce ma ta ya yafe ma ta sannan ya ba ta damar gabatar da kan ta a matsayin mai neman aiki kuma aka tattauna da ita kamar kowa.

Cece-kuce ya yawaita akan yadda ya yi saurin yafe ma ta

Labarin nan ya janyo cece-kuce kwarai a kafafen sada zumunta, inda wa su su ke ganin be dace ya yafe ma ta cikin sauki ba.

Read also

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

Wani Chizurum James ya ce:

“Share duk wasu mutanen da su ke tambayar ka dalilin da ya sa ka kara ba ta dama. Kullum mu na neman dama daga Ubangiji kuma kullum ya na yafe mana, amma yanzu kusan kowa ba ya da zuciyar yafiya, amma ya na so Ubangiji ya yafe ma sa. Ka yi abinda ya dace Ikechukwu Diamond. Duk mai yafiya ya na tare da rahamar Ubangiji.”

Temitope Olajide ya ce:

“Gaskiya Ikechukwu Diamond ka burge ni. Amma ta yi maka alkawarin biyan ka kudin da ta damfare ka? Kuma a haka za ka mika mata dukiyar kamfani? Ina mamakin yadda za ka ba ‘yar damfara dama a karo na biyu.”

Motunrayo Ojomo ta ce:

“Ikechukwu Diamond, me zai sa ka ba barauniya dama ta zo ta sa ka a matsala ta kuma zubar ma ka da mutunci? Akan me? Ko ka tabbatar ta tuba? Na yi mamakin yadda bayan shekaru 5 kuma take a nan ka yafe mata.”

Read also

Pandora: EFCC ta yi wa Peter Obi kiran gaggawa kan kamfanoninsa na ketare

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari.

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Source: Legit.ng

Online view pixel