Yana da hatsari: FG ta yi gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya kan hada katin SIM da NIN

Yana da hatsari: FG ta yi gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya kan hada katin SIM da NIN

  • An gargadi 'yan Najeriya da kada su yarda a hada lambarsu ta dan kasa da katin wani daban
  • A cewar gwamnatin tarayyar, an yi hakan ne domin ba ainahin mai lambar NIN din kariya daga afkawa cikin matsala
  • Da take ci gaba da bayani, FG ta ce tunda abu ne mai sauki gano duk wani laifi da aka aikata da wannan sim din za a alakanta shi zuwa ga ainahin mai lambar NIN din

Abuja - Hukumar sadarwa ta Najeriya ta aika da wani sako zuwa ga ‘yan Najeriya.

Hukumar ta bukaci ‘yan Najeriya da kada su yarda a hada lambarsu ta dan kasa da katin sim din wani daban, jaridar Punch ta rahoto.

Yana da hatsari: FG ta yi gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya kan hada katin SIM da NIN
Yana da hatsari: FG ta yi gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya kan hada katin SIM da NIN
Source: Original

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Daraktan NCC, Efosa Idehen.

Read also

Bidiyon otal a kasan ruwa wanda ake biyan N28m na kwana 1 ya janyo cece-kuce

Da yake magana kan amfanin hada NIN da Sim, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kada wani dalili yasa kamfanin sadarwa ya bari wani mutum na daban yayi rijistar Sim da lambar NIN din wani."

A cewarsa, an bayar da wannan shawarar ne don kare ainahin mai lambar NIN din daga duk wasu matsaloli da zai taso daga amfani da SIM din wani.

Jaridar ta kuma nakalto yana cewa:

"Idan mutanen, wadanda aka hada SIM dinsu da layinku, suna amfani da SIM dinsu don aikata laifi ko kowane irin ta'asa, cikin sauki za a gano shi zuwa gare ku, za a hukunta ku saboda SIM din yana da alaka da NIN din ku."

FG ta ce an hada layukan waya miliyan 180 da NIN

A gefe guda, mun kawo a baya cewa mataimakin shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) Farfesa Umar Danbatta, ya bayyana adadin layukan wayar tarho da aka hada da Lambar Shaida ta Ƙasa (NIN) a yanzu. A cewarsa, sama da layukan waya miliyan 180 aka hada a yanzu.

Read also

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

Ya bayyana hakan a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, jaridar The Nation ta rahoto.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa ya fadi wannan ne biyo bayan yiwa 'yan Najeriya sama da miliyan 60 rijista da Hukumar samar da lambar dan Kasa (NIMC) ta yi a cikin bayanan NIN.

Source: Legit.ng

Online view pixel