Rikicin majalisar malaman Kano: Daga karshe Sheikh Ibrahim Khalil ya magantu

Rikicin majalisar malaman Kano: Daga karshe Sheikh Ibrahim Khalil ya magantu

  • Sheikh Ibrahim Khalil ya magantu a kan rikicin majalisar malaman jihar Kano wanda ya kai ga dakatar da shi a matsayin Shugaba
  • Shehin Malamin ya bayyana hakan a matsayin wata jarrabawa daga Allah domin ya ga karfin imaninsa a matsayinsa na Musulmi
  • Ya kuma yi godiya ga dukkanin mutanen da suka tsaya tsayin daka don ganin kawunan malaman sun hadu waje daya

Jihar Kano - Daga karshe Sheikh Ibrahim Khalil ya magantu bayan barkewar rikici wanda ya kai ga dakatar da shi daga matsayin shugaban majalisar malamai na jihar Kano.

Sheikh Khalil ya bayyana rikicin a matsayin nufin Allah, wanda ya ce ya gwada shi domin ya ga karfin imaninsa a matsayinsa na Musulmi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wakilin Birtaniya ya dira kotu domin shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB

Rikicin majalisar malaman Kano: Daga karshe Sheikh Ibrahim Khalil ya magantu
Rikicin majalisar malaman Kano: Daga karshe Sheikh Ibrahim Khalil ya magantu Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Malamin ya yi magana ne a Kano a ranar Asabar, 23 ga watan Oktoba, lokacin da ya karbi bakuncin Majalisar Tabbatar da Shari’a a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta rahoto a baya cewa majalisar malamai ta jihar Kano, ta dakatar da shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil,

Majalisar ta bayyana dakatar da babban malamin ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a jihar Kano.

An kuma maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, a matsayin shugaban rikon kwarya.

Sai dai kuma, dakatarwar ta hadu da turjuya daga malamai daban-daban a jihar.

Amma da yake magana a ranar Asabar, Sheikh Khalil ya ce:

“Allah ya yi alkawari gwada mu a komai. Abun da ya faru shakka babu abu ne da Allah ke so ya yi amfani da shi don ganin karfin imaninmu a tafarkinsa.

Kara karanta wannan

Hakimi a Yobe ya hadu da fushin gwamna bayan da ya narkawa gwamnan ashariya

“Ina kallon hakan a matsayin gwaji, amma nagode Allah ya nuna mana duk daya muke, amma duk haka muna neman yafiyar Allah.
“Ina kuma godiya ga dukkan wadanda suka tsaya tsayin daka don ganin an samu hadin kai, ciki harda wadanda ma ba malamai bane.
“Irin haka abu ne da muke alfahari da shi. Zan ci gaba da nuna godiya ga dukkan wadanda suka nuna damuwa da kuma wannan majalisa ta Shariah.”

Da yake jawabi a madadin Majalisar Shari’ar, Malam Jamilu Mu’azu Haidar, ya ce sun zo Kano ne a madadin kungiyar ta kasa, don nuna goyon bayansu ga shugabancin Khalil.

Haidar wanda ya kasance mamba a Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya ce sun saurari bayanai daban-daban kan rikicin sannan an ba su tabbacin cewa babu hannun gwamnatin jihar a ciki.

Ya ce:

“Muna kira ga sauran malamai da su ji tsoron Allah su dawo a ci gaba da tafiya tare, kamar yadda Sheikh Khalil yake kokarin yi.

Kara karanta wannan

Rikici a APC yayin da aka rantsar da 'yan wani tsagi bayan taron gangami a Ribas

“Majalisar malaman na amfana daga ilimi da shugabancinsa fiye da yadda yake amfana daga gare ta.”

Kano: Sabon rikici ya barke a majalisar malamai, wasu sun yi fatali da dakatar da Khalil

A gefe guda, bayan majalisar malamai ta Kano ta dakatar da Sheikh Ibrahim Khalil tare da maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, wata kungiyar malamai ta jihar Kano ta nisanta kanta daga wannan sanarwar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, majalisar malaman ta ce ta dakatar da malamin ne kan zarginsa da siyasantar da lamurran majalisar.

Amma, a takardar da kungiyar ta sanar wacce sakataren ta, Dr Sa'idu Ahmad Dukawa ya fitar, ta ce ba su da hannu a wannan hukuncin na dakatarwan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel