Wakilin Birtaniya ya dira kotu domin shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB

Wakilin Birtaniya ya dira kotu domin shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB

  • Wakilin Birtaniya na Najeriya ya tsinkayi kotu inda ya isa domin sauraron shari'ar Nnamdi Kanu
  • Tariq Ahmad, karamin ministan harkokin waje na Birtaniya, ya ce su na son jin yadda aka dawo da Kanu Najeriya
  • Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da Kanu gaban kotu ne kan laifuka 7 da ake zarginsa ciki har da cin amanar kasa

FCT, Abuja - Wakilin Birtaniya a Najeriya ya isa babbar kotun tarayya da ke Abuja domin sauraron shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu.

TheCable ta ruwaito cewa, wakilin Ingilan ya isa farfajiyar kotun a wata mota fara kirar Toyota Highlander wurin karfe takwas da minti uku na safiyar ranar Alhamis.

Wakilin Birtaniya ya dira kotu domin shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB
Wakilin Birtaniya ya dira kotu domin shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kanu wanda ke da shaidar zama dan kasar Birtaniya, ya shiga hannun hukuma a Najeriya ne a watan Yuni kuma an dawo da shi gida Najeriya domin a gurfanar da shi kan zargin cin amanar kasa da ake masa.

Kara karanta wannan

Shugaban Turkiyya ya gargadi Buhari, ya ce ya kula da masu shirin juyin mulki

Ya tsere Ingila a shekarar 2017 bayan ya tsallake belin da aka bada shi, TheCable ta wallafa.

Tariq Ahmad, karamin ministan harkokin waje na Birtaniya, ya ce Ingila ta na bukatar bayanin Najeriya kan yadda ta cafke Kanu.

A yayin da ya ke Ingila, ya kafa wata daba ta 'yan awaren IPOB wadanda ke da "burin dakatar da dukkan ayyukan laifi da farmakin 'yan ta'adda a kasar Biafra", kamar yadda Emma Powerful, mai magana da yawun kungiyar 'yan awaren yace.

Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya ce jami'an tsaron farin kaya sun hana wanda ya ke karewa neman dauki daga Ingila.

Za a sake gurfanar da shugaban kungiyar masu tada kayar bayan a raba kasar nan ne a yau kan wasu laifuka bakwai da ake zarginsa da su da suka hada da cin amanar kasa da kuma ta'addanci.

Kara karanta wannan

‘Yan Najeriya na fama da yunwa, talauci da rashin tsaro – Sheikh Dahiru Bauchi ya koka

Jami’an DSS, ‘yan sanda, sojoji sun kewaye kotun Abuja a shari’ar Nnamdi Kanu

A wani labari na daban, jaridar TheCable ta ruwaito cewa, an girke jami’an tsaro da yawa a babbar kotun tarayya da ke Abuja don shari’ar Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra ta IPOB.

An ga jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), rundunar sojan Najeriya da jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya suna gadin kowace kofar shiga kotun da titunan da ke shiga ginin kotun.

Ba a bar 'yan jaridar da sunayensu ba sa cikin jerin shirye-shiryen ba a kusa da harabar kotun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel