Majalisar Malaman Kano ta dakatar da Sheikh Khalil daga shugabanci saboda abu biyu

Majalisar Malaman Kano ta dakatar da Sheikh Khalil daga shugabanci saboda abu biyu

  • Majalisar malaman addinin musulunci ta jihar Kano ta dakatar da shugabanta, Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabanci
  • Majalisar da ta haɗa malaman Izala, Tijjaniyya da Kadiriyya, ta amince da ɗaukar wannan matakin ne saboda abu ɗaya
  • Malaman Kano sun zargi tsohon shugaban da saka siyasa, tuni suka maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan

Kano - Majalisar malamai ta jihar Kano, ta dakatar da shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Majalisar ta bayyana dakatar da babban malamin ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a jihar Kano.

Legit.ng Hausa ta gano cewa tuni majalisar ta maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, a matsayin shugaban rikon kwarya.

Sheikh Ibrahim Khalil
Majalisar Malamai ta jihar Kano ta dakatar da Sheikh Khalil daga shugabanci saboda ya yi abu daya Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Saboda me malaman Kano suka dakatar da shi?

Malaman Kano sun zargi tsohon shugaban majalisar ne da saka siyasa a harkokin tafiyar da shugabancin majalisar malamai.

Kara karanta wannan

2023: Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakanan kuma sun zargi malamin da amfani da majalisar wajen cimma wasu muradai na ƙashin kansa.

Manyan malaman Kano daga sanannun ƙungiyoyin addinin musulunci uku, Izala, Tijjaniya da kuma Khadiriyya, sune suka sanar da wannan matakin a wurin taron manema labarai a Kano.

Waye sabon shugaba, Pakistan?

Kafin naɗinsa, Farfesa Pakistan, shine shugaban ƙungiyar Jama'atul Izalatil Bidi'a Wa Iƙamatus Sunnah (JIBWIS), wacce akafi sani da Izala, reshen jihar Kano.

A wani labarin na daban kuma Yan sakai, waɗanda gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya haramta sun kashe wani limami da wasu mutum 10

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutanen ne baki ɗayansu a kasuwa, yayin da wasu huɗu suka jikkata.

Wani ɗan uwan limamin da aka kashe, yace ba abinda ɗan uwansa ya yi sai kawai dan yakasance Bafullatani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel