Kano: Sabon rikici ya barke a majalisar malamai, wasu sun yi fatali da dakatar da Khalil

Kano: Sabon rikici ya barke a majalisar malamai, wasu sun yi fatali da dakatar da Khalil

  • Wata kungiyar malamai ta jihar Kano ta yi watsi tare da nisanta kanta da dakatar da Sheikh Ibrahim Khalil
  • Kamar yadda takardar da ta samu sa hannun wasu manyan malaman Kano ta nuna, sun ce ba su da hannu cikin wannan hukuncin
  • Malaman sun sanar da cewa su masu assasa zaman lafiya da hadin kan Musulmi ne, don haka a kwantar da hankula a jihar

Kano - Kasa da sa'o'i 24 bayan majalisar malamai ta Kano ta dakatar da Sheikh Ibrahim Khalil tare da maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, wata kungiyar malamai ta jihar Kano ta nisanta kanta daga wannan sanarwar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, majalisar malaman ta ce ta dakatar da malamin ne kan zarginsa da siyasantar da lamurran majalisar.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

Kano: Sabon rikici ya barke a majalisar malamai, wasu sun yi fatali da dakatar da Khalil
Kano: Sabon rikici ya barke a majalisar malamai, wasu sun yi fatali da dakatar da Khalil. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Amma, a takardar da kungiyar ta sanar wacce sakataren ta, Dr Sa'idu Ahmad Dukawa ya fitar, ta ce ba su da hannu a wannan hukuncin na dakatarwan.

Takardar ta kara da cewa, kungiyar ta kasance mai neman zaman lafiya tare da hadin kai tsakanin Musulmi a jihar, inda ta ja kunnen cewa wannan hukuncin na iya tabarbara wasu lamurra.

Ta kara da kira ga mazauna jihar Kano da su kwantar da hankulansu tare da yin watsi da duk wani lamari da zai iya kawo tashin-tashina, Daily Trust ta wallafa.

Sauran wadanda suka saka hannu kan takardar sun hada da fitattun malamai kamar su Farfesa Musa Muhammad Borodo, Sheikh Kariballah Sheikh Nasiru Kabara, Sheikha Abdulwahab Abdallah, Farfesa Mohammed Babangida Mohammad, Dr. Bashir Aliyu Umar, Imam Nasiru Mohammad Adam da Dr. Bashir Mu'azzam Mai Bushira.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun kashe sojoji, sun raunata janar, sun yi awon gaba da motocin soji

Ganduje ya sake korar tsohon kwamishinansa, Mu'az Magaji, daga mukaminsa

A wani labari na daban, a karo na biyu a cikin shekara daya, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kori Injiniya Mu'azu Magaji wanda aka fi sani da Dansarauniya, daga mukamin da ya nada shi.

Da farko, gwamnan ya sallami Magaji yayin da ya ke kwamishina bayan ya yi wata wallafar jin dadi kan mutuwar Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya rasu sakamakon cutar korona da yayi fama da ita.

Amma kuma, bayan watanni kadan, Ganduje ya sake bai wa Magaji wani mukami, Daily Trust ta ruwaito. An nada shi a matsayin shugaban aikin bututun iskar gas da kuma kwamitin masana'atun na jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel