Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da yaya da kanwarta

Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da yaya da kanwarta

  • 'Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu yara biyu 'yan gida daya a Akure, babban birnin jihar Ondo
  • Maharan sun sace yaran ne a cikin motar mahaifiyarsu a lokacin da take kokarin bude kofar shiga harabar gidansu
  • Rundunar 'yan sandan jihar Ondo, ta tabbatar da afkuwar lamarin inda tace an tura jami'ai domin ceto yaran da kama masu laifin

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wasu kananan yara biyu daga motar iyayensu a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Channels TV ta rahoto cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 8:00 na dare a yankin Leo da ke birnin, a ranar Juma'a, 22 ga watan Oktoba.

Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da yaya da kanwarta
Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da yaya da kanwarta Hoto: NPF
Asali: Twitter

Maharan sun kai hari ne a mashigin gidan lokacin da mahaifiyar yaran ke bude kofa domin shiga harabar gidansu.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: ‘Yan bindiga sun cinna wuta a fadar sarkin Imo

An tattaro cewa masu garkuwan sun zo ne a cikin wata mota, inda suka kwace makullin mota daga hannun mahaifiyar yaran, sannan suka tsere da motar yayin da suka bar tasu a wajen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'ar hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Ondo, DSP Funmilayo Odunlami ta tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talbijin na Channels a ranar Asabar, 23 ga watan Oktoba.

Ta bayyana cewa mahaifiyar yaran ta kai rahoton lamarin ga 'yan sanda sannan jami'an da ke yake da masu garkuwa da mutane suka shiga aiki a kokarinsu na ceto yaran da kama masu laifin.

Bayan watanni 4 hannun yan bindiga, daliban Birnin-Yauri 27 sun kubuta

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa dalibai da Malaman makarantar sakandaren gwamnatin tarayya FGC, Birnin Yauri, jihar Kebbi, guda 27 da Malami uku sun samu kubuta daga hannun tsagerun yan bindigan da suka sace su.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi arangama da matasa a Imo, an ƙone gidaje da dama

Wadannan Dalibai da Malamai sun sha ne bayan sama da kwanaki 118 hannun yan bindiga.

DailyTrust ta ruwaito cewa Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, ya bayyana hakan ga manema labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel