Da duminsa: Bayan watanni 4 hannun yan bindiga, daliban Birnin-Yauri 27 sun kubuta

Da duminsa: Bayan watanni 4 hannun yan bindiga, daliban Birnin-Yauri 27 sun kubuta

  • Bayan sama da kwanaki 120, wasu cikin daliban Yauri sun samu kubuta
  • Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sako mutum 30; dalibai 27, Malamai 3
  • Yanzu saura sama da dalibai 60 hannun yan bindigan cikin daji

Kebbi - Dalibai da Malaman makarantar sakandaren gwamnatin tarayya FGC, Birnin Yauri, jihar Kebbi, guda 27 da Malami uku sun samu kubuta daga hannun tsagerun yan bindigan da suka sace su.

Wadannan Dalibai da Malamai sun sha ne bayan sama da kwanaki 118 hannun yan bindiga.

DailyTrust ta ruwaito cewa Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, ya bayyana hakan ga manema labarai.

Da yake sanar da hakan a ranar Alhamis, Gwamnan Atiku Bagudu, ya bayyana cewa daliban sun yi hakuri su dauki wannan matsayin jarrabawa

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Bayan kimanin kwanaki 120, Dogo Giɗe ya sako ɗaliban Yauri 28 da malamansu biyu da ke hannunsa

“Annabawan Allah, wadanda su ne zababbun Allah, su ma Allah Ya jarrabe su; amma duk mutumin Allah Ya jarrabe shi ya yi hakuri tabbas ladarsa a wurin Allah ba ta da iyaka.”

Ya kara da cewa wadanda aka sako din sun hada da dalibai mata 2 da maza 25, sai malamai maza biyu da mace daya.

Gwamnan ya bayyana cewa sauran daliban dake hannun yan bindiga kuma ana cigaba da kokarin kubutar da su.

Ya yi addu'an Allah ya taimaka wajen gano sauran.

Gwamnan ya kuma ba da umarnin a duba lafiyar daliban da malaman nasu da aka sako sannan a ba su tallafin da suke bukata kafin a mika su ga iyalansu.

Da duminsa: Bayan kimanin kwanaki 120 hannun yan bindiga, daliban Birnin-Yauri sun kubuta
Da duminsa: Bayan kimanin kwanaki 120 hannun yan bindiga, daliban Birnin-Yauri sun kubuta
Asali: Original

Harin makarantar Kebbi abun damuwa ne, barazana ne ga tsaro a arewa maso yamma – El-rufai

Kara karanta wannan

Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa

Nasir el-Rufai, gwamnan Kaduna, ya ce sace yara ‘yan makaranta da aka yi kwanan nan a Kebbi ba alama mai kyau ba ne ga lamarin tsaro a arewa maso yamma.

El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kaiwa Atiku Bagudu, gwamnan Kebbi.

A ranar 17 ga watan Yuni, wasu ‘yan bindiga sun kai hari Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri, Kebbi, suka yi awon gaba da dalibai da malamai da dama.

Kawo yanzu, jami'an tsaro sun kubutar da mutane 11 daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.

Da yake magana a Kebbi, el-Rufai ya nuna bakin ciki kan harin, sannan ya yi kira da a dauki matakan gaggawa don magance matsalar rashin tsaro a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel