Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwarsa har lahira a Bauchi

Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwarsa har lahira a Bauchi

  • Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta damke wani mutum bisa zargin kashe budurwarsa
  • An tattaro cewa matashin ya gano budurwar tasa tana fitowa daga gidan wani mutum, don haka sai kishi ya dibe shi
  • Wannan ya haddasa cece-kuce a tsakanin masoyan inda shi kuma ya ture ta sannan ta buga kai kasa wanda shine yayi ajalinta

Bauchi - Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Enoch Yohanna bisa zargin ture budurwarsa, Ruth Amos har lahira.

Kakakin ‘yan sandan na jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, 22 ga watan Oktoba, ya ce wasu jami’ai da ke sintiri, sun gano budurwa kwance malele cikin jini, rahoton The Nation.

Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwar sa har lahira a Bauchi
Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwar sa har lahira a Bauchi Hoto: The Nation
Asali: UGC

Hakazalika sun same ta da raunuka a kanta sannan jini na ta bulbulowa daga bakinta a yankin Sabon Kaura da ke garin Bauchi.

Kara karanta wannan

Zargin kashe-kashe: Rundunar ‘yan sanda ta yi karin haske kan rikicin iyakar Bauchi da Gombe

An bayyana cewa a wannan rana da lamarin ya afku, Enoch ya hango marigayiyar tana fitowa daga gidan wani mutumi sai kishi ya debe shi, inda ya kalubalanceta, wannan ne ya kai ga musayar yawu a tsakaninsu.

A cikin haka ne sai ya ture ta sannan sai kanta ya bugu da kasa.

Jawabin ya bayyana cewa bincike da aka gudanar kan al’amarin, ya nuna cewa marigayiyar da Yohanna suna soyayya ne kuma harma sun haifi yara biyu kafin mutuwarta.

Wanda ake zargin mai shekaru 27, wanda ke zaune a Gwallameji Doka, da kanshi ya amsa laifinsa bayan kama shi.

Sanarwar ta ce:

"A ranar 07/10/2021 da misalin karfe 0445hrs wata tawagar sintiri na hadin gwiwa tare da kwamitin tsaro kan zamanm lafiya yayin da suke sintiri sun gano wata matashiya kwance cikin jini da raunuka a kanta sannan jini na ta zuba daga bakinta a Sabon Kaura, tawagar suka kwashe ta zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi, inda likita ya tabbatar da mutuwarta.

Kara karanta wannan

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

"A yayin bincike, an gano cewa wata Hajara Amos mai shekaru 56 a kauyen Bayara ita ce mahaifiyar marigayiyar sannan aka gano sunan marigayiyar a matsayin Ruth Amos mai shekaru 28."

Rundunar 'yan sandan ta ce ana gudanar da bincike, kuma a kwanan nan za a tura wanda ake zargin zuwa kotu, Daily Post ta kuma rahoto.

Soyayya ruwan Zuma: Wata kyayyawar budurwa ta harbe saurayinta har lahira saboda ya ƙi sumbatar ta

A wani labarin na daban, wata budurwa a ƙasar Amurka ta ɗirkawa saurayi harbi har lahira saboda ya ƙi ya sumbace ta.

Aminiya ta rahoto cewa, kyakkyawar budurwar ta nemi saurayin ya sumbace ta amma sam ya ƙi cika mata bukatarta.

Lamarin ya faru ne yayin da muaten biyu suke tsaka da holewarsu a gidan saurayin, suna shan barasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel