Soyayya ruwan Zuma: Wata kyayyawar budurwa ta harbe saurayinta har lahira saboda ya ƙi sumbatar ta

Soyayya ruwan Zuma: Wata kyayyawar budurwa ta harbe saurayinta har lahira saboda ya ƙi sumbatar ta

  • Wata budurwa a jihar Illinois ta ƙasar Amurka ta bindige wani saurayi har lahira saboda ya ƙi sumbatar ta
  • Rahoto ya nuna cewa kyakkyawar budurwan ta nemi saurayin ya sumbace ta har sau biyu amma yana ƙi, hakan ya fusata ta
  • Yan sanda na cigaba da tsare budurwar da ta aikata wannan aiki har zuwa sanda za'a kammala bincike

United States - Wata budurwa a ƙasar Amurka ta ɗirkawa saurayi harbi har lahira saboda ya ƙi ya sumbace ta.

Aminiya ta rahoto cewa, kyakkyawar budurwar ta nemi saurayin ya sumbace ta amma sam ya ƙi cika mata bukatarta.

Lamarin ya faru ne yayin da muaten biyu suke tsaka da holewarsu a gidan saurayin, suna shan barasa.

Soyayya ruwan Zuma
Soyayya ruwan Zuma: Wata kyayyawar budurwa ta harbe saurayinta har lahira saboda ya ƙi sumbatar ta Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Budurwan mai suna Claudia Resendiz-Florez, yar shekara 28 ta ɗauki wannan matakin ne bayan ta nemi saurayin ya sumbace ta amma sai ya juya ya sumbaci wata budurwarsa.

Kara karanta wannan

Auran matar aure, tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda lamarin ya faru

Budurwar ta nuna masa fushi bayan ƙin sumbatar ta a karo na farko da ta nema, sannan ta ce ya zama wajibi ya yi abinda take so a karo na biyu.

Da saurayin yaƙi yin abinda take so a karo na biyu, nan take ta fusata, ta ɗakko bindigarsa dake ajiye a gefe guda ta harbe shi a ƙirji.

Rahoto ya bayyana cewa saurayin bai jima ba ya ƙarasa mutuwa kasancewar harsashin bindigar a ƙirji ya same shi.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Jami'an yan sanda sun cafke budurwar bayan samun rahoton abinda ya faru, kuma suna cigaba da gudanar da bincike.

Ɗan sandan dake jagorantar lamarin ya tabbatar da cewa za'a cigaba da tsare budurwar har zuwa lokacin da Alƙali zai yanke mata hukunci.

A wani labarin kuma mun kawo muku Hotunan Amarya da Ango da suka je wurin ɗaura aurensu a cikin tukunyar girki

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga uku: Rukunin karshe na sabbin jiragen yaƙin 'Super Tucano' sun iso Najeriya

Bisa tilas wata amarya da da angonta suka yi amfani da tukunyar girki wajen tsallake wuraren da ambaliyar ruwa ta mamaye yayin zuwa wurin ɗaura aurensu a ƙasar Indiya.

Hotunan waɗannan ma'aurata ya ƙaraɗe kafafen sada zumunta domin sun yi abin mamaki kasancewar ambaliyar ruwa ta mamaye tituna a gabashin Indiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel