Shugaban kasa daga arewa maso gabas zai kawo karshen ta’addanci - Gwamna Fintiri

Shugaban kasa daga arewa maso gabas zai kawo karshen ta’addanci - Gwamna Fintiri

  • Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya bayyana mafita ga lamarin tashe-tashen hankula a kasar
  • Fintiri ya ce idan har wani dan takara daga yankin arewa maso gabas ya zama shugaban kasa, toh lallai zai kawo karshen ta'addanci a zangonsa na farko
  • Gwamnan na PDP ya ce mai daki shine ya san inda yake yoyo

Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya bayyana cewa zabar shugaban kasa daga yankin arewa maso gabas zai kawo karshen ta’addancin da yankunan kasar ke fuskanta.

Fintiri, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Farfesa Maxwell Gidado, ya bayyana hakan ne a taron karramawa na mujallar North East Star na 2021, inda aka bashi lambar yabo a matsayin gwamnan shekarar.

Shugaban kasa daga arewa maso gabas zai kawo karshen ta’addanci - Gwamna Fintiri
Shugaban kasa daga arewa maso gabas zai kawo karshen ta’addanci - Gwamna Fintiri Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana cewa ta’addanci a arewa maso gabas zai zo karshe a zangon farko na shugabancin kowani dan takara daga arewa maso gabashin kasar, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan IPOB sun kai hari ofishohin yan sanda 164, sun kashe jami'ai 175, duka laifin Nnamdi Kanu ne: FG

A cewarsa, Shugaba daga Arewa maso Gabas zai fahimci halin da ake ciki kuma zai magance lamarin cikin sauki, Naija News ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa tsohon shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya yi iya bakin kokarinsa wajen kokarin kawo karshen ta’addanci.

Sai dai ya ce kokarin Buratai ya haifar da nasarori kadan ne saboda yaki da ta’addancin bai samu goyon bayan da ake bukata ba dari bisa dari daga fadar shugaban kasa.

Fintiri ya ce:

“Za a kawo karshen ‘yan ta’addan Boko Haram a zangon farko na shugaban kasa daga arewa maso gabas. Masu hikimar zance kan ce mai daki shi ya san inda yake yoyo. Laftanal Janar Buratai ya yi iya bakin kokarinsa lokacin da yake jagorantar lamura.
“Da an bashi goyon baya dari bisa dari, toh da ya yi waje da ‘yan ta’addan da ke Sambisa.”

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya hannun yan daba a majalisar dokokin jihar Zamfara

PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri

A wani labarin, Ahmadu Fintiri, ya ce jam’iyyar People Democratic Party (PDP) na bukatar mutane masu mutunci domin kula da harkokinta.

A cewar Fintiri, ta hakan ne kadai babbar jam’iyyar adawar za ta iya lashe zaben shugaban kasa a 2023, jaridar The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, a wajen taron jam’iyyar gabannin babban taronta na kasa da aka shirya yi a ranar 30 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel