PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri

PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri

  • Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya shawarci jam'iyyar PDP kan abubuwan da ya kamata tayi domin kwace mulki a 2023
  • Fintiri ya ce babbar jam'iyyar adawar kasar na bukatar mutane masu mutunci domin yin nasara a babban zabe mai zuwa
  • Ya bayyana hakan ne gabannin babban taron jam'iyyar da za a yi a ranar 30 ga watan Oktoba

Abuja - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ce jam’iyyar People Democratic Party (PDP) na bukatar mutane masu mutunci domin kula da harkokinta.

A cewar Fintiri, ta hakan ne kadai babbar jam’iyyar adawar za ta iya lashe zaben shugaban kasa a 2023, jaridar The Cable ta ruwaito.

PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri
PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, a wajen taron jam’iyyar gabannin babban taronta na kasa da aka shirya yi a ranar 30 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a Abuja, Fintiri ya ce PDP za ta gyara kura-kuran da tayi a baya idan aka bata damar jagorantar kasar a 2023.

Ya ce:

“Duk mun san abubuwan da ke faruwa kamar yadda babban sakataren labaranmu na kasa da kansa ya bayyana - yadda muke cikin matsala a matsayinmu na kasa.
“Muna gab da tsallaka kuma dole muyi abun da ya kamata, tun daga wannan babban taron don tabbatar da ganin cewa mun zabi kwararru da za su jagorance mu da kwarewarsu da mutuncinsu domin ‘yan Najeriya su fara yarda da mu.
“Ya zama dole mu gyara dukkan kura-kuran da muka yi a baya. Shugabanninmu sun yarda cewa mun yi kuskure kuma mun ba ‘yan Najeriya hakuri.

Kara karanta wannan

2023: Mun shirya tsaf don yin kaca-kaca da APC a Zamfara, mataimakin gwamna

“Kuma da wannan, ina ganin akwai bukatar mu hada mutane masu mutunci domin su kula da harkokin jam’iyyar da kuma bamu damar nasara a zaben 2023, musamman kujerar shugaban kasa.”

Gwamnan ya kuma ce sai an hada kai da fata domin kai jam’iyyar ga matakin nasara.

Nasarar jam'iyyar PDP na hannun yan Najeriya a zaɓen 2023, Inji Atiku

A gefe guda, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana yaƙininsa cewa yan Najeriya zasu sake miƙa ragamar mulkin Najeriya ga jam'iyyar PDP a 2023.

Atiku ya roƙi yan siyasa su girmama dokokin zaɓen jam'iyya da kuma kundin tsarin mulkin ƙasa yayin gudanar da kowane irin zaɓe.

Punch ta rahoto tsohon mataimakin shugaban yana cewa matuƙar ana son ɗorewar demokaraɗiyya to sai an tabbatar da ingancin zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel