Yan IPOB sun kai hari ofishohin yan sanda 164, sun kashe jami'ai 175, duka laifin Nnamdi Kanu ne: FG

Yan IPOB sun kai hari ofishohin yan sanda 164, sun kashe jami'ai 175, duka laifin Nnamdi Kanu ne: FG

  • Gwamnatin tarayya ta lissafa laifukan da zata daurawa Nnamdi Kanu a kotu
  • Shugaban kungiyar na IPOB ya gurfana gaban kotu ranar Alhamis
  • Ministan Shari'a ya bayyana adadin jami'an gwamnatin da yan IPOB suka kashe

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta gabatar da binciken da ta gudanar kan ayyukan ta'addancin da yan kungiyar awaren kafa kungiyar IPOB suka yi a fadin tarayya.

Gwamnati tace kawo yanu, yan ta'addan sun kai hare-hare ofishohin yan sanda 164 kuma sun babbaka wasu, rahoton Premium Times.

Antoni Janar na kasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya bayyana hakan a jawabin da ya sakewa manema labarai ranar Juma'a, 22 ga Oktoba, 2021.

Ya kara da cewa a wadannan hare-hare, yan ta'addan sun kashe jami'an yan sanda 175.

Gwamnatin ta kara da cewa yan IPOB sun kai hare-hare ofishohin hukumar gudanar da zabe ta INEC 19 kuma sun kona motocin hukumar 18.

Malami yace za'a daura laifin dukkan wannan kan shugaban kungiyar, Nnamdi Kanu, wanda ke tsare yanu hannun hukumar DSS, riwayar TVC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan IPOB sun kai hari ofishohin yan sanda 164, sun kashe jami'ai 175, duka laifin Nnamdi Kanu ne: FG
Yan IPOB sun kai hari ofishohin yan sanda 164, sun kashe jami'ai 175, duka laifin Nnamdi Kanu ne: FG Hoto: Aso Villa
Asali: UGC

Kada ku sake wani abu ya hana zaben gwamnan Anambra, Shugaba Buhari ga Hafsoshin tsaro

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya umarci shugabannin tsaro su tabbatar babu wani abu da ya hana zaɓen gwamnan jihar Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Mai bada shawara kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (Mai ritaya), shine ya sanar da haka ga manema labaran gidan gwamnati jim kaɗan bayan hitowa daga taron tsaro.

Monguno yace shugaba Buhari ya bada wannan umarnin ne domin martani kan yawaitar ƙalubalen tsaro a jihar Anambra, wanda ƙungiyar aware IPOB ke ɗaukar nauyi.

Monguno yace:

"Shugaban ƙasa ya bada umarnin a kowane hali kada a sake wani abu ya hana samun nasarar gudanar da zaɓen. Mutane na da damar zaɓen shugabannin su."
"Babu wata tawaga ko ƙungiya da za'a bari su tada yamutsi, wanda ka iya jawo asarar rayuka."

Asali: Legit.ng

Online view pixel