Kada ku sake wani abu ya hana zaben gwamnan Anambra, Shugaba Buhari ga Hafsoshin tsaro

Kada ku sake wani abu ya hana zaben gwamnan Anambra, Shugaba Buhari ga Hafsoshin tsaro

  • Shugaba Buhari ya umarci hukumomin tsaro su yi duk mai yuwuwa wajen tabbatar da an gudanar da zaɓen gwamnan Anambra
  • Buhari yace duk matakin da ya kamata a ɗauka, domin tabbatar da ai baiwa mutane tsaro sun zaɓi shugabannin su
  • Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi, yace rundunar yan sanda zata tabbatar da tsaro a Anambra da sauran sassan ƙasar nan

Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya umarci shugabannin tsaro su tabbatar babu wani abu da ya hana zaɓen gwamnan jihar Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Mai bada shawara kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (Mai ritaya), shine ya sanar da haka ga manema labaran gidan gwamnati jim kaɗan bayan hitowa daga taron tsaro.

Dailytrust ta rahoto cewa ranar Alhamis ɗin nan da muke ciki, an gudanar da taron tsaro bisa jagorancin shugaba Buhari a fadarsa dake Abuja.

Read also

Kada ku bar masu tsattsauran ra'ayin addini su kwace iko da Najeriya, Sarkin Musulmi ga Jami'an tsaro

Taron tsaro a fadar shugaban ƙasa
Kada ku sake wani abu ya hana zaben gwamnan Anambra, Shugaba Buhari ga Hafsoshin tsaro Hoto: Buhari Sallau FB Fage
Source: Facebook

Meyasa shugaba Buhari ya ɗauki wannan mataki?

Monguno yace shugaba Buhari ya bada wannan umarnin ne domin martani kan yawaiyar ƙalubalen tsaro a jihar Anambra, wanda ƙunguyar aware IPOB ke ɗaukar nauyi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Channesl tv ta rahoto Monguno yace:

"Shugaban ƙasa ya bada umarnin a kowane hali kada a sake wani abu ya hana samun nasarar gudanar da zaɓen. Mutane na da damar zaɓen shugabannin su."
"Babu wata tawaga ko ƙungiya da za'a bari su tada yamutsi, wanda ka iya jawo asarar rayuka."
"Shugaban ƙasa ya shaidawa shugabannin tsaron cewa su tabbatar da an yi zaɓen ko da kuwa za'a jibge jami'an tsaro ne a kowane sashi na jihar."

Bugu da ƙari yace a watannin da suka shuɗe, jami'an soji sun samu nasara sosai a yaƙin da suke da matsalar tsaro a kudu maso gabas.

Read also

Rikicin APC a Jihar Kano: Gwamna Ganduje Ya Yi Tsokaci Kan Matakin da Suke Dauka da Tsagin Malam Shekarau

Zamu tabbatar da zaman lafiya a Anambra - Yan sanda

Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi, wanda yana cikin mahalarta taron, ya bayyana yaƙininsa cewa rundunar yan sanda zata tabbatar da tsaro a Anambra da sauran sassan ƙasar nan.

"Mun tattauna akan zaɓen jihar Anambra dake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba, ina mai tabbatar wa mutanen jihar Anambra da yan Najeriya baki ɗaya cewa gwamnati ta shirya gudanar da zaɓen."
"Za'a gudanar da sahihin zaɓe kuma zamu tabbatar an tsare rayukan al'umma. Wannan kaɗai ce hanyar tabbatar da demokaradiyya da kyakkyawan shugabanci."

A wani labarin kuma Yan sanda sun fara bincike kan yadda jami'an tsaro suka kaɗa kuri'a a zaben APC na tsagin Ganduje

Wasu hotunan bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wani ƙaramin sufetan yan sanda ya kaɗa kuri'a a zaɓen APC na Kano.

Mataimakin sufetan yan sandan ƙasar nan mai kula da shiyya ta ɗaya, Abubakar Sani Bello, ya bada umarnin bincike.

Read also

Hotunan yadda 'yan sanda suka yi ram da masu zanga-zanga a Lekki Tollgate

Source: Legit.ng

Online view pixel