Yan Daba Ɗauke da Makamai Sun Kai Hari Wurin Gangamin Taron Atiku a Kaduna

Yan Daba Ɗauke da Makamai Sun Kai Hari Wurin Gangamin Taron Atiku a Kaduna

  • Wasu 'yan daba da ake zaton ɗaukar nauyinsu aka yi sun kai hari filin da PDP ta shirya kamfen Atiku a Kaduna
  • Mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya nuna rashin jin daɗinsa da faruwar lamarin
  • Atiku ya roki shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gaggauta daukar mataki domin kamfen ya gudana lami lafiya

Kaduna - Rahoton da muke samu ya nuna cewa wasu yan Daba sun farmaki magoya bayan PDP a Ranches Bees Stadium, Kaduna, wurin gangamin taron ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya tabbatar da faruwar lamarin a wani rubutu da ya saki a shafinsa na dandalin Facebook ranar Litinin.

Wurin taron PDP a Kaduna.
Yan Daba Ɗauke da Makamai Sun Kai Hari Wurin Gangamin Taron Atiku a Kaduna Hoto: OfficialPDPNigeria
Asali: Facebook

Atiku ya yi kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da ya umarci sauran jam'iyyu su dakatar da mambobinsu daga yunkurin ta da yamutsi a wurin taron.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka Da Kukan Tsadar Abinci, Farashin Kayayyaki A Najeriya Ya Kara Tashi Da Kaso 20.77

"Yanzu nake samun labarin cewa wasu yan daba da aka ɗauki nauyinsu sun kai wa magoya bayan PDP hari da zummar ta da hargitsi da tarwatsa taron kamfen PDP a jihar Ƙaduna."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wannan ya saɓa wa Demokaraɗiyya kuma ya saɓa wa yarjejeniyar zaman lafiya da jam'iyyu suka rattaɓa wa hannu makonni kalilan da suka shuɗe."
"Ina rokon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kira jam'iyyu su gaggauta dawo da magoya bayansu cikin hayyacinsu domin tabbatar da an yi kamfe da zaɓen kansa cikin kwanciyar hankali da sahihanci."

- Atiku Abubakar.

Atiku ya ɗaukar wa arewa Alkawari a Kaduna

A wani labarin kuma Manyan Alkawurra Uku da Atiku Ya Daukar Wa Jagororin Arewa a Kaduna

Atiku Abubakar ya yi alkawarin magance matsalar tsaro da ya addabi yankin arewa idan ya ɗare shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Ba Da Mamaki, Ta Lashe Zaben Ciyamomi 30 da Kansiloli a Wata Jiha

Ɗan takarar kujera lamba ɗaya a inuwar PDP yace ya shirya tsaf wajen tsamo tattalin arzikin kasar nan daga durkushe wa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel