Ambaliya: Ku Aje Kamfe Mu Taimaka Wa Mutane, Peter Obi Ga Sauran Yan Takara

Ambaliya: Ku Aje Kamfe Mu Taimaka Wa Mutane, Peter Obi Ga Sauran Yan Takara

  • Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya gana da gwamna Ortom domin shirya zuwansa Benuwai da ziyartar wuraren da Ambaliya ta taba
  • Ɗan takarar shugaban kasa a LP ya yi kira ga takwarorinsa na APC, PDP, NNPP da sauransu su haɗa hannu da shi don tallafawa mutane
  • A watanni biyu da suka gabata, Ambaliya ta raba miliyoyin mutane da Mahallansu, wasu daruruwa sun mutu

Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi kira ga takwarorinsa su dakatar da yaƙin neman zaɓe kana su haɗa hannu da shi domin tallafawa mutanen da Ibtila'in Ambaliyar ruwa ta shafa a ƙasar nan.

Channels tv tace Mista Obi ya yi wannan kiran ne yayin da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, a gidansa dake Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan Goyon Bayan Gwamna APC, Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Yuwuwar Wike Ya Fice PDP

Masu neman zama shugaban kasa a 2023.
Ambaliya: Ku Aje Kamfe Mu Taimaka Wa Mutane, Peter Obi Ga Sauran Yan Takara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yayin ziyarar, Obi da gwamnan Ortom sun tattauna kan yadda zai kai ziyara wuraren da Ambaliyar ta shafa a jihar Benuwai dake Arewa ta tsakiya da sauran wasu jihohi.

Tsohon gwamnan Anambra na cikin masu tseren gaje Buhari tare da Bola Ahmed Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP, Rabiu Kwankwaso na NNPP da sauran su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obi yace yana tsammanin yan takarar shugaban ƙasan su nuna damuwarsu ga bayin Allah da Ibtila'in ya afka mawa idan aka yi la'akari da miliyoyin da suka ƙashe wajen sayen Fom ɗin takara.

Legit.ng Hausa ta gano cewa matsalar Ambaliyar ruwa ta jawo asara da dama a sassan wasu jihohin Najeriya cikin watanni biyu da suka gabata.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta ce kusan mutane miliyan Biyu da rabi lamarin ya shafa yayin da Ambaliyar ta kashe mutum 603.

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Wane jihohin Ibtila'in ya shafa a Najeriya?

Ruwa ya shanye gidaje da Gonakin mutane a jihohin Legas, Yobe, Borno, Taraba, Adamawa, Edo, Delta, Kogi, Neja, Filato, Benuwai, Ebonyi, Anambra, Bauchi, da Gombe.

Sauran jihohin da Ambaliyar ta shafa sune Kano, Jigawa, Zamfara, Kebbi, Sokoto, Imo, Abiya da kuma babban birnin tarayya, Abuja.

A wani labarin kuma Jigon PDP Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Peter Obi a 2023

Jigon jam'iyyar PDP mai adawa a kasar nan, Dr Sampson Orji, ya bayyana cewa Peter Obi ne zabinsa a babban zaben 2023.

Orji, wanda ya nemi tikitin takarar gwamnan Abiya a inuwar PDP, yace Atiku abokinsa ne amma Obi ya fi shi cancanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel