Harin Goronyo: Shugaban soji ya isa Sokoto, ya nemi sojoji da su rubanya kokarinsu

Harin Goronyo: Shugaban soji ya isa Sokoto, ya nemi sojoji da su rubanya kokarinsu

  • Watakila kasancewar shugaban hafsan soji, Janar Faruk Yahaya a jihar Sokoto ya aika da sako mai karfi ga 'yan fashin
  • Yahaya ya kasance a kasuwar Goronyo da ke jihar Sokoto a ziyarar aiki bayan harin baya-bayan nan da 'yan bindiga suka kai wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da yawa
  • Shugaban soji ya bukaci dakarun da su kara kaimi wajen aiwatar da ayyukansu a yankin, don kawo karshen irin wadannan hare-haren

Sokoto - Biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai kan kasuwar Goronyo a jihar Sokoto wanda yayi sanadiyar kisan mutane 40, shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Faruk Yahaya a ranar Litinin, ya fara ziyarar aiki a yankin.

Faruk ya bukaci rundunar sashi na 8 da ke da alhakin kula da yankin da su rubanya kokarinsu wajen fatattakar ‘yan ta’adda daga sansaninsu da mabuyarsu, rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro raguwa yake yi ba karuwa ba, ku sauya labarinku: Buhari ya aika sako ga manema labarai

Harin Goronyo: Shugaban soji ya isa Sokoto, ya nemi sojoji da su rubanya kokarinsu
Harin Goronyo: Shugaban soji ya isa Sokoto, ya nemi sojoji da su rubanya kokarinsu Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Shugaban sojin ya yi umurnin ne yayin da gwamnan na jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa hare-haren da aka kai kan kauyen Goronyo abun takaici ne.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa akwai bukatar sake duba dabarun aiki tare da aika karin sojoji a yankin domin guje ma sake faruwar haka a gaba, Channels Tv ta ruwaito.

A nasa bangaren, Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci shugaban sojin da ya tattara duk wasu albarkatu da ke hannunsa don tunkarar makiyan jihar.

Da yake magana a yayin wani ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan, Laftanal Janar Faruk Yahaya ya ba da tabbacin cewa rundunar sojin ba za ta ba gwamnati da mutane kunya ba, yayin da ake kokarin sake sauya ayyuka a arewa ta yamma.

Kara karanta wannan

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

Ya jadadda cewa rundunar na aiki kai da kai da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki don fuskantar lamarin.

Ya yaba ma gwamna Tambuwal kan goyon bayan da yake ci gaba da rundunar soji sannan ya bukace shi da kada yayi kasa a gwiwa a kokarinsa.

A hedkwatar sashi na 8, shugaban sojin ya karbi bayanai kan lamarin tsaro a Sokoto da jahohin da ke makwabtaka daga babban kwamanda, Manjo Janar Uwem Bassey.

Ya yaba ma jami’ai da sojojin sashin kan jajircewarsu sannan ya bukace su da su rubanya kokarinsu a yaki da fashi da makami.

Ya baiwa sojojin tabbacin cewa a shirye yake ya samar da kayan aikin da suka dace domin gudanar da ayyukan su.

Game da jin dadin sojoji, shugaban sojin ya tabbatar da cewa za su gina karin gidaje don jami’an, ta kara da cewa za a kuma samar da kayan sojoji.

Miyagun yan bindiga sun sake bude wa mutane wuta a kasuwar jihar Sokoto

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

A wani labarin, mun kawo a baya cewa wasu miyagun yan bindiga sun kai hari kasuwar garin Goronyo dake ƙaramar hukumar Goronyo, a jihar Sokoto.

Wata majiya daga garin ta bayyana cewa yan ta'addan sun kai hari da adadi mai yawa na mutane ranar Lahadi da daddare, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Rahoto ya nuna cewa har zuwa yanzun ba'a san adadin yawan mutanen da harin ya shafa ba, amma mutane da dama sun mutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel