Rashin tsaro raguwa yake yi ba karuwa ba, ku sauya labarinku: Buhari ya aika sako ga manema labarai

Rashin tsaro raguwa yake yi ba karuwa ba, ku sauya labarinku: Buhari ya aika sako ga manema labarai

  • Shugaban kasa Buhari ya taya daukacin al’umman Musulmi da ‘yan Najeriya baki daya murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad
  • A sakonsa, shugaban kasar ya magantu kan lamarin rashin tsaro wanda ya kasance daya daga cikin tarin matsalolin da kasar ke fuskanta
  • Don haka an bukaci kafofin watsa labarai da su magance lamarin ta hanyar rahotannin da suke yadawa

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce rashin tsaro na raguwa ne a yanzu, kuma lokaci yayi da kafafen watsa labarai za su canja sigar kawo rahoton cewa yana karuwa.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan a ranar Litinin, 18 ga watan Oktoba, a wani sako don murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad.

Rashin tsaro raguwa yake yi ba karuwa ba, ku sauya labarinku: Buhari ya aika sako ga manema labarai
Rashin tsaro raguwa yake yi ba karuwa ba, ku sauya labarinku: Buhari ya aika sako ga manema labarai Hoto: Femi Adesina
Source: Facebook

A wata sanarwa da hadimin shugaban kasa Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nakalto shugaban kasar yana cewa:

Read also

Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba

“Lokaci ya yi da za mu canza maganar karuwar matsalar tsaro da raguwar matsalar tsaro a kasar.”

Muna nasara a yakin

A cewarsa, akwai karuwar ayyuka a bangaren rundunar soji, da sauran hukumomin tsaro da na leken asiri don magance matsalolin tsaro a kasar.

Buhari ya bukaci kafofin watsa labaran da su magance yadda za su dunga kawo rahotannin tsaro da matakan tsira a yayin da suka zo nazarin lamarin hauhawan rashin tsaro da saukarsa.

Shugaban kasar ya ce gwamnatinsa na samun nasara a kan ta’addanci da sauran laifuka da taimakon al’umman kasar wadanda ke bada hadin kai da karfafa hukumar ‘yan sanda, tsaro da shugabancin sojoji.

Gaisuwar zaman lafiya

Da yake taya Musulmai da 'yan Najeriya baki daya murna, shugaban kasar ya aika da gaisuwar zaman lafiya, hadin kai da fatan alheri.

Read also

Sabon rikici ya barke tsakanin mazauna Benue da Ebonyi, an sanya dokar ta baci

Shugaba Buhari ya yi kira ga Musulmi da su kasance masu yafiya da hakuri sannan su yi koyi da koyarwa Annabi Muhammadu wanda ake bikin zagayowar haihuwarsa.

Buhari ya fusta da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwananakinku sun kusa karewa

A gefe guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan bindiga cewa su kasance a shirye don murkushe su ya zo kusa.

Shugaban ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin 18 ga watan Oktoba yayin da yake mayar da martani kan kisan sama da mutane 30 a Goronyo, Jihar Sakkwato ranar Lahadi.

Buhari, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, ya ce kwanakin 'yan bindiga a kirge suke saboda karfin da sojojin Najeriya ke samu ta hanyar samun kayan aiki da sauran bukatu.

Source: Legit.ng

Online view pixel