Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

  • Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar ragargazar wasu 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
  • Yanayin ya faru ne yayin da 'yan ta'addan ke kokarin kwace garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno
  • An kashe akalla 'yan ta'adda 20 tare da rasa jaruman sojojin Najeriya hudu a wannan mummunan bata-kashi

Borno - Sahara Reporters ta ruwaito cewa, akalla sojojin Najeriya uku da mayakan Boko Haram 20 sun rasa rayukansu a ranar Asabar yayin da sojoji ke kokarin kwato garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

An ce maharan sun mamaye jerangiyar gidajen 777, a wajen birnin Maiduguri da misalin karfe 10:15 na daren Asabar.

Wani rahoton daban ya ce an gaggauta tura jirage masu saukar ungulu na rundunar sojin sama don hana maharan kwace yankin.

An fafata tsakanin sojojin Najeriya da 'yan ta'addan Boko Haram, an ragargaji Boko Haram
'Yan ta'addan Boko Haram | Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

Yayin da sojoji ke fafatawa da masu tayar da kayar baya, mazauna Pompomari, jerin gidajen 778 da 1000 sun kasance cikin shiri.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan ta'adda da shugabannin 'yan bindiga 12 da aka sheke a 2021

Lamarin ya faru ne sa’o’i bayan da sojojin Najeriya a mahadar Banki, da ke yankin Kumshe a jihar suka ragargaji kwanton bauna da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi.

Hakazalika, an kashe sojoji uku da 'yan ta'adda 20 a wani lamarin na daban da ya faru da misalin karfe 07:45 na daren Juma'a.

An kwace makamai daban-daban da tabarmi na mayakan.

Kungiyar Boko Haram da reshenta, SWAP sun kashe dubban mutane tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Rundunar sojan Najeriya ta sha yin ikirarin cewa an ci galaba kan masu tayar da kayar baya.

Rahotanni sun bayyana cewa, dubban 'yan ta'addan sun mika wuta ga hukumomin tsaro na soji a yankuna daban-daban na jihar Borno.

A baya kadan, rahoto daga jaridar TheCable ta bayyana cewa, yankin Boko Haram, ISWAP ta hallaka shugaban Boko Haram Abubakar Shekau.

Kara karanta wannan

Daukar aikin sojin sama: Abubuwa 14 da wadanda aka zaba suke bukatar tanada nan kusa

Boko Haram sun kashe sojoji, sun raunata janar, sun yi awon gaba da motocin soji

A wani labarin, Wasu 'yan ta'adda daga kungiyar Boko Haram da ke hade da kungiyar ISWAP a ranar Lahadin da ta gabata sun kai hari kan wata rundunar soja da ke a yankin Ngamdu, garin kan iyaka tsakanin Borno da Yobe.

A wannan mummunan harin, sun kashe sojoji sama da 6 kamar yadda majiyoyin soji suka shaida wa SaharaReporters.

Ngamdu gari ne a karkashin karamar hukumar Kaga ta jihar Borno kuma kusan kilomita 100 zuwa babban birnin Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel