Da Duminsa: Miyagun yan bindiga sun sake bude wa mutane wuta a kasuwar jihar Sokoto

Da Duminsa: Miyagun yan bindiga sun sake bude wa mutane wuta a kasuwar jihar Sokoto

  • Yan bindiga sun sake kai hari kasuwar garin Goronyo, a jihar Sokoto, karo na uku cikin mako biyu
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi, inda suka kashe mutane da dama
  • Yan bindiga na cigaba da tserowa zuwa jihar Sokoto daga Zamfara, inda jami'an sojoji ke luguden wuta ta sama da ƙasa kan yan ta'addan

Sokoto - Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari kasuwar garin Goronyo dake ƙaramar hukumar Goronyo, a jihar Sokoto.

Wata majiya daga garin ta bayyana cewa yan ta'addan sun kai hari da adadi mai yawa na mutane ranar Lahadi da daddare, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Rahoto ya nuna cewa har zuwa yanzun ba'a san adadin yawan mutanen da harin ya shafa ba, amma mutane da dama sun mutu.

Read also

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Hari a kasuwar Goronyo jihar Sokoto
Da Duminsa: Miyagun yan bindiga sun sake bude wa mutane wuta a kasuwar jihar Sokoto Hoto: Daular Usmaniya FB fage
Source: Facebook

Wannan harin shine karo na uku cikin mako biyu da yan bindiga suka kai wata kasuwa a jihar Sokoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani rubutu da shafin Daular Usmaniyya ta buga a dandalin Facebook, ta jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa.

Wani sashin rubutun yace:

"Muna mika ta'aziyya ga al'ummar musulmi na jahar Sokoto, musamman na Karamar Hukumar Goronyo akan Ibtala'in da ya faru na kisan kan mai uwa da wabi da 'yan bindiga sukayi a kasuwar Goronyo."

Yan bindiga sun kashe mutum 20

A farkon wannan watan ne, wasu tsagerun yan ta'adda suka hallaka aƙalla mutum 20 a kasuwar Ungwan Lalle, ƙaramar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto.

Sojoji sun kwashe makonni da dama suna aikin ruwan wuta ta sama da ƙasa kan sansanin yan bindiga a jihar dake makotaka da Sokoto, wato Zamfara.

Read also

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari jami'ar Arewa, Sun yi awon gaba da dalibai

Tun bayan ɗaukar matakai a Zamfara, yan bindiga suka fara gudun hijira suna kafa sansani a Sabon Birni, inda suka matsawa mutanen ƙauyuka.

A wani labarin kuma mun kawo muku Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa yan fashin daji sun fara sako mutanen da suka kama saboda babu abincin ba su.

Dakta Abdullahi Shinkafi, mataimakin kwamitin tsaro, yace matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka suna haifar da ɗa mai ido.

Source: Legit.ng News

Online view pixel