Daukar aikin sojin sama: Abubuwa 14 da wadanda aka zaba suke bukatar tanada nan kusa

Daukar aikin sojin sama: Abubuwa 14 da wadanda aka zaba suke bukatar tanada nan kusa

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta zabi mutanen da za ta fara horarwa a shirin shiga aikin sojin sama
  • Rundunar ta soji ta bayyana sunayen mutanen da ta zaba domin fara shiga wannan horo nan da karshen Oktoba
  • Hakazalika, ta bayyana abubuwan da ake bukata kowane cikin wadanda aka zaba zai tana da kafin lokacin horon

Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara don samun horo na Basic Military Training Course (BMTC 42/2021) daga cikin wanda suka nuna sha'awar shiga aikin sojin sama.

AVM Mahmud Nda Madi ne ya rattaba hannu kan jerin sunayen da aka fitar a madadin babban hafsan sojin sama sannan aka yada a shafin Facebook na NAF a ranar Asabar 16 ga watan Oktoba.

Daukar aikin sojin sama: Abubuwa 14 da wadanda aka zaba suke bukatar tanada
Sojin saman Najeriya | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

An nemi wanda suka yi nasarar da su zo domin fara karbar horo a Cibiyar Horar da Sojojin Najeriya da ke Kaduna ranar Asabar, 30 ga Oktoba, 2021.

Kara karanta wannan

Gwamnoni, jiga-jigan APC, PDP 7 da EFCC ke bincika kan batun Pandora Papers

Madi ya yi ishara da cewa za a iya samun jerin sunayen wadanda suka yi nasara a kafar yanar gizo ta sojojin saman Najeriya: www.nafrecruitment.airforce.mil.ng.

Abubuwan da ake bukata wadanda aka zaba su tanada

1. Kananan riguna fafare guda 2 (T-shirts)

2. Gajerun wanduna guda 2 masu launin shudi

3. Takalma sau-ciki na motsa jiki, farare guda 2

4. Fararen safa guda 3

5. Kayan sakawa na al'adun kasa da aka amince dasu kala 3

6. Fararen riguna guda 2

7. Madaurin wuya guda 1

8. Wanduna guda 2 masu launin baki

9. Karin kayan sakawa gama-gari kala 3

10. Takunkumin fuska da za a iya wankewa guda 4

11. Man wanke hannu mai kashe kwayar cuta mai yawan 200ml

12. Hotunan fasfo guda 4

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

13. Kwafin takardar shaidar BVN

14. Bakin man goge takalmi, burushi, kayan aski da kayan wanka

Sojin sama ta dawo da shirin daukar daliban sakandare kai tsaye zuwa aikin soja

A wani labarin, Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) ta sake gabatar da shirin daukar daliban da suka kammala makarantar sakandare ta soji kai tsaye a matsayin sojan sama, The Guardian ta ruwaito.

Babban Hafsan Sojojin Sama (CAS), Air Marshall Isiaka Amao ne ya bayyana hakan, a wurin faratin yaye dalibai na 36 na Makarantar Sojojin Sama da ke Jos ta Jihar Filato.

Amao ya ce wasu daga cikin daliban da suka nuna sha’awa kafin su shiga cikin shirin daukar kai tsaye an tura su rundunonin NAF daban-daban a fadin kasar bayan sun sami horo a Cibiyar Horar da Sojoji da ke Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel