Gwamnoni, jiga-jigan APC, PDP 7 da EFCC ke bincika kan batun Pandora Papers

Gwamnoni, jiga-jigan APC, PDP 7 da EFCC ke bincika kan batun Pandora Papers

Zargin wasu fitattun 'yan Najeriya kamar yadda takardun Pandora suka bayyana ya sa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta fara gudanar da cikakken bincike kan zargin.

Takardun da aka ce wasu takardu ne da wasu gungun 'yan jarida na duniya suka buga sun zargi wasu fitattun 'yan siyasar Najeriya da jami'an gwamnati wadanda tuni aka fara binciken su da nufin tabbatar da ikirarin da ake yi musu.

Takardun Pandora basu tsaya kan jami'an gwamnati da 'yan siyasar Najeriya kadai ba, sun kunshi sunaye da yawa na fitattun mutane a duniya a kasashe 91, inji ICIJ.

Pandora Papers: Jerin gwamnoni, jiga-jigan APC, PDP da ke fuskantar binciken EFCC
Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Daga cikin fitattun 'yan Najeriya, galibin wadannan mutane ana tuhumar su ne da mallakar kadarorin sirri a kasashen waje wadanda aka same su ta haramtacciyar ribar harkalla.

Kara karanta wannan

Daukar aikin sojin sama: Abubuwa 14 da wadanda aka zaba suke bukatar tanada nan kusa

Jerin wadanda EFCC ta fara bincike akansu

Rahoton da jaridar Punch ta bayar ya bayyana sunayen wadanda ake zargi kamar kuma EFCC ta fara bincike akansu:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

  1. Peter Obi (PDP)
  2. Mohammed Bello-Koko (MD na NPA)
  3. Stella Oduah (APC)
  4. Gwamna Abubakar Bagudu (Kebbi)
  5. Gwamna Gboyega Oyetola (Osun)
  6. Bola Tinubu (Shugaban APC na kasa)
  7. Gwamna Dapo Abiodun (Ogun)

Asirin fitattun ‘Yan siyasa da 'Yan kasuwan Najeriya 10 ya tonu a badakalar Pandora Papers

A tun farko, ‘Yan siyasa 336 aka tona asirin barnar da suke tafkawa kamar yadda binciken International Consortium of Investigative Journalists ya nuna. Kungiyar ICIJ ta ‘yan jarida da suka kware wajen bincike sun wallafa badakalar Pandora Papers da ya tona wa wasu ‘yan siyasa a Najeriya asiri.

Punch tace takardun da aka fitar sun bayyana cewa akwai fitattun manyan da ake ganin darajarsu a cikin wadanda suke aikata ba daidai ba.

Kara karanta wannan

Pandora Papers: An sake bankaɗo manyan kamfanonin gwamnan APC na 3 na ƙasar waje

‘Yan jarida 600 suka hadu suka yi wannan bincike da ya fallasa asirin mutane a kasashen Afrika takwas, daga ciki har da ‘yan Najeriya har goma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel