Mun yi amfani da aikin noma wajen tsamo sama da mutum milyan hudu daga Talauci, Ministan Noma

Mun yi amfani da aikin noma wajen tsamo sama da mutum milyan hudu daga Talauci, Ministan Noma

  • Ministan Noman Najeriya ya bayyana adadin wadanda suka fito daga kangin talauci cikin shekaru biyu da suka gabata
  • Ministan wanda ya gaji Sabo Nanono ya bayyana irin ayyukan da ma'aikatar keyi
  • Ya ce nan da shekaru 10 lallai za'a fidda mutum milyan 100 daga talauci

Abuja - Gwamnatin tarayya a ranar Juma'a ta bayyana cewa kimanin mutane milyan hudu da dubu dari biyu ta tsamo daga cikin matsanancin talauci ta aikin noma cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ministan Noma da raya karkara, Mohammed Mahmoud, ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai da aka shirya don murnar ranar abinci ta duniya 2021 a Abuja.

Ya bayyana cewa an samu cimma hakan ne ta hanyoyin tallafi da dama da aka baiwa manoma da yan kasuwan kayan masarufi.

Read also

Dan majalisa ga FG: Makuden kudi kafintoci da direbobi ke samu, a wajabta musu haraji

Ya jaddada niyyar Shugaba Muhammadu Buhari na tsamo mutum milyan 100 daga cikin talauci.

A cewarsa:

"Ta hanyar shirye-shiryen tallafi da kuma noma da kasuwancin kayan masarufi, mun tsamo jimillar mutum 4,205,576 daga talauci cikin shekaru biyu da suka gabata."
"Zamu cigaba da wannan saboda yana cikin manufofin shugaban kasa a alkawarin da yayi na tsamo yan Najeriya milyan 100 daga cikin talauci cikin shekaru 10."

Mun yi amfani da aikin noma wajen tsamo sama da mutum milyan hudu daga Talauci, Ministan Noma
Mun yi amfani da aikin noma wajen tsamo sama da mutum milyan hudu daga Talauci, Ministan Noma Hoto: Noma
Source: UGC

A sashen ilmantar da mutane kan harkar noma, Ministan ya ce gwamnati ta horas da manoma, matasa, maza da mata 2,205,576 kan ilmin noma kuma an tallafa musu, kuma wannan shiri na cigaba da gudana.

Ministan ya kara da cewa sashen noma zai cigaba da bada gudunmuwa wajen inganta tattalin arzikin GDP na Najeriya daga 23% zuwa 50% nan da shekaru goma.

Read also

Duk da komawa APC, da alamu Fani-Kayode zai fuskanci fushin kotu saboda badakala

Mun rabawa matasan Najeriya 7,057 tallafin N3bn ta shirin NYIF, CBN

A bangare guda, babban bankin Najeriya (CBN), yace a shirin da yake yi tare da ma'aikatar matasa da wasanni, kawo yanzu an rabawa matasan Najeriya 7,057 kudi N3bn.

An yiwa shirin take 'Asusun lamunin matasan Najeriya' (NYIF).

Wannan na kunshe cikin rahoton da CBN ya wallafa a shafinsa ranar Litinin, 11 ga Okotba, 2021.

A cewar rahoton, wadanda suka amfana da wannan kudi sun hada da daidaikun mutane 4,411, da kuma masu kananan sana'o'i 2,646.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel